Gwamna Wike Ya Sake Martani Kan Rikicin PDP, Ya Faɗi Aikin Da Zai Wa APC
- Gwamnan Jihar Ribas, Nyesome Wike, ya caccaki wasu 'ya'yan PDP dake sukarsa, ya nemi su maida hankali kan cin zabe
- Wike ya bayyana cewa shi da 'yan tawagarsa sun maida hankali wajen ganin bayan APC reshen jihar Ribas
- Har yanzun, masu faɗa a ji na jam'iyyar PDP sun gaza sulhunta gwamnan da ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya caccaki jiga-jigan PDP dake sukarsa, inda ya bayyana cewa a lokacin da suka maida hankali kan kalamai mara dadi, shi kuma yana kokarin ganin bayan APC a Ribas.
A ranar Litinin da ta gabata, Wike ya yi ikirarim cewa babu wanda zai razana shi domin zai yi duk abinda ya natsu cewa dai-dai ne ko da kuwa za'a masa taron dangi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamna Wike shi ne Jagaba a rikicin da har yau aka gaza lalubo hanyar kawo ƙarshensa a jam'iyyar PDP.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da yankin Ogbunabali Sand-filled a Patakwal ranar Talata, gwamnan ya bayyana cewa ya kudiri aniyar rushe jam'iyyar APC a jihar Ribas.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kuma nuna ɓacin ransa kan yaddda mutane ke sukar sunansa a jihohin su, inda ya ƙara da cewa ba abinda zai ɗauke masa hankali yayin da yake kokarin ruguza tsarin APC a jihae dake kudu maso kudancin Najeriya.
Wike ya ce:
"Maimakon ku maida hankali kan yadda jam'iyyar PDP zata samu nasara a zaɓe, a'a kun koma yawo kuna biyan kudi a gidan Talabijin kuna magana kan Wike kowace rana."
"A halin yanzu Wike da 'yan tawagarsa sun maida hankali kan rushe baki ɗaya ginin APC, samar da ayyukan demokaradiyya ga kowa. Kai kuma a jiharka mahaifarka kana ta ɓaɓatu a kan Wike."
Komawar Shekarau PDP Albarka ce ga NNPP - Galadima
A wani labarin kuma Tsohon Na Hannun Daman Buhari Ya Magantu Kan Sauya Shekar Shekarau Zuwa PDP
Jigon jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, Buba Galadima, ya ce sauya shekar Shekarau Albarka ce ga jam'iyyarsu.
Galadima, wanda a baya yana ɗaya daga cikin makusantan Buhari, ya ce Shekarau ya saba cewa an zalunce shi ya fice daga jam'iyya.
Asali: Legit.ng