Gwamnatin Gombe Ta Rusa Ofishin Yakin Neman Zaben Dan Takarar Gwamna Na PDP

Gwamnatin Gombe Ta Rusa Ofishin Yakin Neman Zaben Dan Takarar Gwamna Na PDP

  • Gwamnatin jihar Gombe ta rushe ofishin kamfen din dan takarar gwamna a PDP da ke hanyar gidan gwamnati
  • Hukuma ta bayyana dalilin rushe ginin da cewa, ofis na kamfen din kusa da hanyar da gwamna ke bi kullum
  • Ana yawan samun takun-saka tsakanin jam'iyyu a jihohi, lamarin da ke tunzura mabiya su kaure da fada

GRA, jihar Gombe - Gwamnatin APC a Gombe ta Inuwa Yahaya, ta rushe ofishin gangamin zaben dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP, Muhammad Jibrin Dan Barde.

Legit.ng Hausa ta gani cewa, an rusa hukumar tsara birni ta GOSUPDA a Gombe ce ta rusa ginin a jiya Talata 30 ga watan Agusta.

A watan Maris din da ta gabata, GOSUPDA ta fara rusa wani shashe na ginin ke kan kwanan Liberty da kusa da gidan gwamnati a hanyar GRA, lamarin da ya jawo cece-kuce.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: ASUU ta gama tattaunawa a Abuja, ta sake fitar da matsaya

Yadda aka rusa ofishin kamfen na dan takarar gwamnan PDP
Gwamnatin Gombe Ta Rusa Ofishin Yakin Neman Zaben Dan Takarar Gwamna na PDP | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa, yayin da jami'an ke rusa ginin, wasu magoya bayan Dan Barde sun samu raunuka sakamakon arangama da suka yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani shaidan gani da ido ya shaida cewa, 'yan sanda sun dira wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 10:30 na safe, inda suka watsa matasan da ke arangama da jami'an.

Ya kuma shaida cewa, bayan watsa jama'a, 'yan sanda da jami'an GOSUPDA din sun yi nasarar rushe wani bangare na ginin.

An saba umarnin kotu

A baya an ruwaito cewa, Dan Barde ya kai kara kotu, inda ya samu takarda daga babban kotun jiha da ta umarci gwamnati ta dakata da batun rusa ginin.

Da yake zantawa da manema labarai, hadimin gwamnan kan harkokin ci gaban gari, Kaftin Peter Bitrus Bilal (Retd), ya ce an rushe ginin ne saboda bai cancanta ya kasance a wurin ba.

Kara karanta wannan

Karfin hali: An kama wani sojan bogi da ke yiwa mata fashi da makami

Ya sam bai kamata a samu ofishin kamfen din jam'iyyar adawa yana kallon masaukin shugaban kasa ba a jihar, wanda kuma hanya ce da gwamna ke bi zuwa ofis a kowace rana.

Ya kuma bayyana cewa, ginin an yi masa rajista a GOSUPDA ne da sunan Gombe Good Leadership Association, kuma an ba shi izinin kasancewa ne na wucin gadi.

Wakilin Legit.ng Hausa a jihar Gombe ya ga yadda wasu ma'aikata ke aikin tattara sauran tarkacen da aka rusa da kuma cire karafan rodi da ke cikin ginin.

Daya daga cikin lebororin, Musa Ahmad da ke aiki ya ce an kawo su ne domin baje kasar wajen, amma bai san ko za a sake gini ne a wurin ba.

Gombe: Bayan shan kaye a APC a 2018, Barde ya dawo PDP, ya samu tikitin gwamna na 2023

A wani labarin, Muhammad Jibril Dan Barde ya lashe tikitin takarar gwamna a jam'iyyar PDP a zaben 2023 a jihar Gombe da aka gudanar.

Kara karanta wannan

Hankali ya tashi yayin da 'yan bindiga suka sace wani dan kasar waje, suka kashe soja a Kaduna

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, jami'in zabe, Mista Mike Oghiadomhe, ya ce Barde, ya samu kuri’u 160 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Dr Jamilu Isyaku Gwamna, wanda ya samu kuri’u 119.

Sauran ‘yan takarar, sun hada da AVM Adamu Shehu Usman (rtd) ya samu kuri’u 18, Dakta Abubakar Ali Gombe, da kuri’u 17, Dakta Babayo Ardo Kumo ya samu kuri’u 13, yayin da Dokta Gimba Ya’u Kumo ya samu kuri’u daya tilo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.