Yadda Malam Shekarau ya Canza Jam’iyya Sau 4 a Shekaru 8 Daga 2014 Zuwa 2022
- Sanatan Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau ya tabbatar da ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP zuwa PDP bayan wata uku
- Kafin yanzu Malam Ibrahim Shekarau ya yi zama a jam’iyyun APC da PDP, amma babu inda ya taba shafe shekaru biyar a jere
- Wannan ne karo na biyar da tsohon Gwamnan zai canza gida a siyasa, kuma karo na biyu da ya tsallaka zuwa jam’iyyar PDP
Mun tattaro lokutan da fitaccen ‘dan siyasa, Malam Ibrahim Shekarau ya sauya-sheka a siyasa tun bayan narkewar ANPP a APC.
1. 2014
A shekarar 2014 ne tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau ya yi watsi da APC da sunan an zalunce su bayan kafa jam’iyyar. Zuwan ‘Yan G7 ya sa shi ya koma PDP.
A wancan lokaci Rabiu Kwankwaso yana Gwamna, sun yi takara a APC yayin da Shekarau suka shiga zabe a jam’iyyar PDP, APC ta karbe mulki daga sama har kasa.
2. 2018
Ana shirin zaben 2019 sai aka ji labari cewa Ibrahim Shekarau ya yi waje daga jam’iyyar PDP a sakamakon ruguza shugabannin jama’iyya na reshen Kano da aka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wannan karo ma, Malam Shekarau ya fita daga jam’iyya ya ba su Rabiu Kwankwaso wuri. APC tayi nasarar karbe tsohon gwamnan, ta sa ya zama Sanata.
3. Mayun 2022
A watan Mayu ne aka ji Ibrahim Shekarau ya fice daga APC, ya shiga jam’iyyar NNPP. Masu nazari sun yi mamakin auren na Sanata Shekarau da Rabiu Kwankwaso.
Kafin a je ko ina sai labari ya fara yawo cewa Malam Shekarau zai canza gida saboda ‘Yan Kwankwasiyya sun mamaye jam’iyyar NNPP, haka kuma za a yi.
4. Agustan 2022
A ranar 29 ga watan Agusta 2022, aka bada sanarwar cewa Sanatan Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau ya dawo PDP, jam’iyyar da ya bari gabanin zaben 2019.
‘Dan siyasar ya yi watsi da takarar Sanatan da aka ba shi a NNPP, ya bi Atiku Abubakar. A nan ma Sardaunan Kano ya yi zargin ba ayi mutanensa adalci ba.
Kano dai ta APC ce - Bashir Ahmaad
Yau ku ka ji labari tsohon Gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau ya yi tsalle zuwa Jam’iyyar PDP daga NNPP, wannan sauyin sheka zai karfafawa PDP a 2023.
Duk da wannan babban kamu, Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmaad yace Jam’iyyar APC da ‘Yan takaranta, Bola Tinubu da Nasiru Gawuna za su doke PDP.
Asali: Legit.ng