PDP ta Karbi Shekarau, Mai ba Buhari Shawara Ya Yi Hasashen Wanda Zai Ci Zaben Kano
- Bashir Ahmaad ya jawo muhawara a shafinsa na Facebook bayan ya yi hasashen jam’iyyar APC ce za ta lashe zabe mai zuwa
- Mai taimakawa shugaban Najeriyan yace APC mai mulki za tayi galaba a zaben shugaban kasa da na Gwamna a Jihar Kano
- Wasu sun yi wa Hadimin shugaban kasan raddi, an kuma samu wadanda suka yarda Bola Tinubu zai doke Atiku Abubakar
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja – A ranar Litinin, 29 ga watan Agustan 2022, Bashir Ahmaad ya takalo abin magana a sanadiyyar nasarar da ya hango jam’iyyar APC ta samu.
A cewar wannan matashin ‘dan siyasa wanda yana cikin masu taimakawa shugaba Muhammadu Buhari, jam’iyyar APC ta lashe zaben jihar Kano a 2023.
Kamar ya yi magana ne a shafinsa na Facebook, yace
Kano is for APC
Kano is for Gawuna
Kano is for Tinubu
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ma’ana:
Kano ta APC ce
Kano ta Gawuna ce
Kano ta Tinubu ce.
- Bashir Ahmaad
Legit.ng Hausa ta kawo rahoto cewa Nasiru Yusuf Gawuna ne wanda zai tsaya takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar APC mai mulki a zaben badi.
Haka zalika Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne yake rike da tutar APC a zaben shugaban kasa.
APC za ta sha kashi a Kano?
Tuni mutane suka shiga maidawa Ahmaad martani, daga ciki akwai masu ganin yanzu lissafi ya canza, domin kuwa babu sunan Muhammadu Buhari a akwatin zabe.
"‘Danuwana kuma Abokina, Bashir Ahmad, Kwankwaso, Atiku da Obo duk su na da rabonsu a Kano. Ya kamata zuwa yanzu ka san wannan…
Inji Jack Obinyan
Amma Ahmaad ya na da ja, yace daukacin masu zabe a jihar Kano za su ba Tinubu kuri’arsu ne.

Kara karanta wannan
Yanzu-Yanzu: Atiku Da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Dira Birnin Kano Kan Sauya Shekar Shekarau

Asali: Twitter
Ibrahim Abbas yace:
Ku na ruwa
Yanzu na gama fada!
- Abdul Danja
In Allah ya yarda Kano ta Atiku ce
- Al Ameen Arsalan
Somin tabi #AtikuOkowa2023
- Sufyan Existing
Peter Obi zai ci zabe
Wannan rabuwar kan za ta kara taimakawa Mai girma Peter Obi. Ku cigaba da rigimarku a Kano.
- Ogomegbunam SuccessJames Nwoye II
Injiniya A S Wudilawa bai goyi bayan Bashir Ahmaad ba, yace APC ta jefa al’umma a halin wayyo Allah.
Ba za mu gane haka ba sai ranar zabe, muna addu’ar Allah ya bamu Gwamna kamar Abba kabir Yusuf, albarkar Annabi Muhammad (SAW)
- B. Jaddah Sharifai
Wani masoyin shugaba Muhammadu Buhari mai suna Sani Lawal Buhariyyah yake cewa:
Insha Allahu Najeriya Sai Malam Ahmad Bola Tinubu; Kano Sai Gawuna.
Maryam Ilyas Gwarzo tana tare da APC, ta rubuta:
GAWUNA SAK
Yadda Bashir Ahmaad bai yi nasara a zaben shiga takara ba, Shu'aibu Abubakar Izge yace Atiku ne zai ci zaben shugaban kasan 2023 a jihar Kano.

Kara karanta wannan
Osinbajo, Lawan, Da Sauran Mutum 20 Da Suka Sayi Fom Din APC Zasu Gana Don Tinubu
In Allah ya so, ko da kujerar majalisar dokoki daya, APC ba za ta samu a Kano ba.
- Othman Mohammed Salisu Gombe
Masu yin shinkafa da wake
Ga yadda abin yake nan:
Najeriya ta Tinubu (APC ce) in Allah ya yarda
Kano ta Abba Gida Gida (NNPP)
Insha'Allah.
Kano ta (APC) ce
Kono ta (NNPP) ce
- Inji Ali Haidar
Najeriya sai ATIKU
KANO sai GAWUNA
- Aminu Abdullahi
Rikicin Wike v Atiku
Dazu kun ji labari wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP sun taso Iyorchia Ayu a gaba, sun ce dole a canza shugaban jam’iyya na kasa.
‘Yan bangaren Wike su na cewa sai an canza shugaban jam’iyya na kasa sannan za su yi sulhu da ‘dan takara, Atiku Abubakar a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng