Rikicin PDP: Wani Abu Zai Faru Nan Ba Da Jimawa Ba, Gwamna Wike

Rikicin PDP: Wani Abu Zai Faru Nan Ba Da Jimawa Ba, Gwamna Wike

  • Gwamnan Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce ba abun da ya faru a jam'iyyar PDP amma nan ba da jimawa ba wani abu zai faru
  • Wike wanda ke takun saƙa da Atiku, ɗan takarar shugaban kasa a PDP ya ce ba abinda zai razana shi wajen yin abinda ya dace
  • Ga dukkan alamu wutar rikicin babbar jam'iyyar hamayya na cigaba da ruruwa duk da yunkurin da wasu ke yi na lalubo hanyar maslaha

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a ranar Litinin, ya sake buɗe baki kan rikicin da ya dabaibaye PDP, ya ce duk abinda ke faruwa ba komai bane amma, "Wani abu zai faru," nan ba da jimawa ba.

A cewar ɗan takarar, wanda ya nemi tikitin shugaban ƙasa a PDP, ba wanda ya isa ya masa barazana domin zai yi abinda yake ganin shi ne dai-dai duk rintsi, kuma duk yadda za'a taru a kansa.

Kara karanta wannan

2023: Da Yawa Cikin 'Yan Takarar Shugabancin Kasa Yashe Najeriya Suke da Buri, Wike

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike.
Rikicin PDP: Wani Abu Zai Faru Nan Ba Da Jimawa Ba, Gwamna Wike Hoto: Nyesom Wike/facebook
Asali: Facebook

Channels tv ta ruwaito cewa Wike ya yi wannan tsokacin ne lokacin ƙaddamar da fara aikin titunan Eneka Internal da ke yankin Obio-Akpor, jihar Ribas.

Gwamna Wike ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duk wanda ya sanni, ya san na riga na yanke hukunci a zuciyata kuma na yi imani cewa abinda na ke yi dai-dai ne, idan kun ga dama ku mun taron dangi."
"Matukar na share kokanto a rai na, zan yi abinda yake na dai-dai a kowane lokaci, ban damu da kowane kalan taron dangin da za'a mun ba."
"Kowanen mu ya kwantar da hankalinsa, kun ji abubuwan da ke faruwa a PDP, ba abinda ya faru har yanzun, amma da ikon Allah wani abu zai faru nan ba da jimawa ba."

Asalin rikicin PDP

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Gwamna Wike ya tsame jikinsa tun bayan da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ɗaɗa shi da ƙasa da sauran ƴan takara a zaben fudda gwanin PDP.

Kara karanta wannan

Babban gaye: Yadda nau'in takalmin wani dan kwalisa ya girgiza mutane a intanet

Haka zalika lamarin ya ƙara tsananta bayan zaɓen gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a inuwar PDP.

Duk da wannan dambarwa da ake ciki a babbar jam'iyyar adawa, Wike ya gana da Peter Obi, mai neman kujerar shugaban kasa a LP, da Bola Tinubu na jam'iyyar APC.

Ya kuma sa labule da ɗaya daga cikin ƴan takarar da suka nemi tikitin APC kuma gwamnan Ebonyi, David Umahi, sannan ya tattauna da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, Jaridar The Cable ta ruwaito.

A ranar Jumu'a, Gwamna Wike ya fito ya gaya wa duniya cewa duk waɗan nan abubuwan da ake ganin yana yi, yana yin su ne domin amfanin ƴan Najeriya.

A wani labarin kuma kun ji cewa wata Kungiya Ta Roki Gwamna Wike Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Koma Bayan Peter Obi a 2023

Wata kungiya ta nemi gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya mance da Atiku da Tinubu, ya mara wa Peter Obi baya a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiyar Mayu Da Matsafa Ta Najeriya Ta Yi Magana Mai Ƙarfi Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na APC

Shugaban ƙungiyar, High Chief Felix Ogbegbor, ya ce Obi yana da tarihin gaskiya kuma ya fi sauran ƴan takara cancanta da kwarewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262