Peter Obi Ya Yi Magana a Kan 'Hada-Kai' da Atiku Bayan An yi Kus-Kus a Landan

Peter Obi Ya Yi Magana a Kan 'Hada-Kai' da Atiku Bayan An yi Kus-Kus a Landan

  • Akwai jita-jitar ‘dan takaran jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sa labule da Peter Obi kwanan nan a kasar ketare
  • Kwamitin yakin zaben Obi/Datti ya fitar da jawabi na musamman, yace Obi bai yi wani zaman yarjejeniya da su Atiku ba
  • Masu magana da sunan jirgin yakin takarar LP a 2023 sun ce ana yada wadannan labarai ne domin tallata wasu ‘yan takara

Abuja - Ofishin yada labaran kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Obi-Datti 2023, sun ce babu wata magana da aka ajiye da Atiku Abubakar.

A ranar Lahadi, Vanguard ta rahoto cewa kwamitin neman zaben takaran Obi-Datti 2023 ya fitar da jawabi game da rade-radin marawa PDP baya a zabe.

A jawabin da aka fitar a Abuja, wannan kwamiti yace makaryata ke yada wannan labari da nufin iyayen gidansu su yi kasuwa a takarar shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

Daga karshe Atiku Abubakar ya yi maganar ‘rigimarsa’ da Gwamna Wike a PDP

Wannan kwamitin yakin neman zabe yace ana kakaba hotunan Obi da sauran ‘yan takara saboda a rabi farin jininsa, amma a gaskiya babu batun hada-kai.

Labarin bogi ne - Obi/Datti

“A maimakon su dage wajen tallata ‘yan takaransu, wadannan miyagun mutane sun koma amfani da ‘dan takararmu domin samu suna a siyasa.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mun fahimci masu wannan sun gagara tallata ‘dan takararsu ne domin bai da abin da ake nema.”
Atiku da su Peter Obi
Atiku da Obi a zaben 2019 Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

“Mun san niyyar wadannan mutane na tallata labarin bogi da cewa ‘dan takaran LP, Peter Obi, ya hadu da takwaransa na PDP, sun shiga yarjejeniya.
“Wannan ba gaskiya ba ne ko ta kusa, ko ta nesa. Wuraren da Obi ya je a kasar waje, da wadanda ya hadu da su, duk ba boyayyun abubuwa ba ne.
“Amma masu yada karyayyaki sun fi sha’awar su kirkiri karya da nufin tallata ‘dan takaransu.”

Kara karanta wannan

Magidanci Mai Mata 4 Da 'Yaya 34 Sun yi Rijistan Zabe, Yace Atiku Duk Zasu Kadawa Kuri'u

Jirgin ceto al'umma

Daily Post tace jawabin ya kara da cewa Peter Obi da Datti Baba Ahmed su na takara ne domin ceto Najeriya, kuma babu abin da zai kauda tunaninsu.

Idan har Obi ya shiga zabe ne da nufin kawo canji, to ba zai hada kai da tsofaffin ‘yan siyasa ba. Jawabin yana nuni ga ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar.

Kamfe a wurin ibada

A yau muka kawo maku rahoto cewa Hukumar zabe ta kasa watau INEC ta ja-junne a kan kamfe a Masallatai da Coci, ana barazanar daure masu saba doka.

Festus Okoye yace dokar zabe na shekarar 2022 ba ta yarda ayi amfani da coci ko masallatai wajen yakin neman zabe ko a tallata wata tafiyar siyasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng