An Raba Kan Shugabannin PDP da Batun Tunbuke Shugaban Jam’iyya daf da 2023

An Raba Kan Shugabannin PDP da Batun Tunbuke Shugaban Jam’iyya daf da 2023

  • Wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP sun taso Iyorchia Ayu a gaba, sun ce dole a canza shugaban jam’iyya na Najeriya
  • ‘Yan bangaren Wike su na cewa sai an sauke shugaban jam’iyya na kasa sannan za su yi sulhu da ‘dan takara, Atiku Abubakar
  • Inda matsalar ta ke, a tsarin mulki, ko Ayu ya bar kujerarsa, Umar Damagum daga yankin Arewa zai zama shugaban PDP

Abuja - A halin yanzu majalisar gudanarwa ta PDP watau NWC, ta rabu a sakamakon kiran da ake yi na sauke shugaban jam’iyya na kasa, Dr. Iyorchia Ayu.

Jaridar Punch ta kawo tahoto a ranar Litinin, 29 ga watan Agusta 2022 wanda ya nuna cewa a cikin ‘Yan NWC, akwai masu goyon bayan a canza shugaba.

Haka zalika akwai bangaren wadanda ba su goyon bayan ayi waje da Iyorchia Ayu daga kujerarsa kamar yadda bangaren Gwamna Nyesom Wike suke so.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPP Ya Fadi Babban Abin da Ya Wargaza Taron Dangin Kwankwaso/Obi

Wani babba a jam’iyyar PDP ya shaidawa jaridar cewa wannan ya jawo rabuwar kai a majalisar NWC.

Akwai cakwakiya a kasa

Wata majiyar ta shaida cewa sauke Ayu ba zai kawo karshen matsalar ba domin ko da an yi waje da shi, Umar Damagum daga Arewa ne zai zama shugaba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda wannan ‘dan jam’iyya ya fada ba tare da ba ya bari an kama sunansa ba, mafita ita ce NEC ta sauke duka ‘Yan NWC, ta nada rikon kwarya.

Shugaban Jam’iyya
Shugabannin PDP na kasa Hoto: abba_kadade
Asali: Twitter

Mutanen Wike sun kafe

Mutanen Gwamnan Ribas wanda ake rigima da shi a PDP, suna goyon bayan jam’iyya ta koma hannun Taofeek Arapaja ne wanda ya fito daga yankin Kudu.

Rahoton yace Arapaja bai taba boye cewa yana tare da Gwamna Seyi Makinde da Nyesom Wike ba. Amma kakakin PDP, Debo Ologunagba yace ba haka ba.

Kara karanta wannan

Daga karshe Atiku Abubakar ya yi maganar ‘rigimarsa’ da Gwamna Wike a PDP

Ologunagba yace ‘yan majalisar NWC su na tare da jam’iyya ne ba wasu gwamnoni ba.

Ologunagba wanda yake magana da yawun bakin jam’iyyar hamayyar yace NWC ta na ganin darajar gwamnoninta, amma PDP ce a gabanta kafin kowa.

Ganin kurarren lokacin da ake da shi, wasu na ganin za iyi wahala a sauke Ayu, sai idan shi ko wasu shugabannin suka zabi su sauka daga mukamansu.

Bukatun su Wike

A can baya kun ji labari cewa mutanen Gwamna Wike suna so Atiku ya sa hannu a yarjejeniyar wa’adi daya idan ya dare kan kujerar shugaban kasa.

Daga cikin bukatun bangaren Gwamnan na Ribas shi ne a ba mutanensa mukamai idan har jam’iyyar PDP tayi nasarar kafa gwamnati a Mayun 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng