Kwankwaso: Zulum Ya Ci Taliyar Ƙarshe, NNPP Za Ta Ƙwace Borno A 2023

Kwankwaso: Zulum Ya Ci Taliyar Ƙarshe, NNPP Za Ta Ƙwace Borno A 2023

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP ya ce jam'iyyarsa za ta ci zabe a Jihar Borno a 2023
  • Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce ya yi imanin NNPP ne za ta ci zaben 2023 a jihar duba da irin dandazon mutanen da suka fito tarbansa
  • Kwankwaso ya yi Allah-wadai da rufe sakatariyar jam'iyyar NNPP da hukumar tsara birane ta jihar Borno ta yi gabanin ziyararsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ayyana cewa jam'iyyarsa za ta kwace mulkin Jihar Borno daga hannun Gwamna Babagana Zulum, da ma wasu jihohi a kasar a 2023.

Kwakwaso ya yi wannan furucin ne a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, jim kadan bayan ya kaddamar da sakatariyar jam'iyyar a ranar Asabar, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Dan Siyasan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Bayyana Dan Takarar Da Zai Gaji Kuri'u Miliyan 12 Na Buhari A Arewa

Sanata Kwankwaso
Kwankwaso: NNPP Za Ta Kwace Borno Daga Hannun Zulum A 2023. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ranar Alhamis, hukumar kula da tsarin birane na Jihar Borno ta rufe sakatariyar amma daga baya gwamnan ya bada umurnin a bude.

Wani sashi cikin jawabin Kwankwaso:

"Ina son tabbatar muku da cewa da izinin Allah idan kuka zabi dan takarar gwamna na NNPP da sanatoci uku, mambobin majalisar tarayya 10 da mambobin majalisar dokokin jiha 28 daga NNPP da kuma dan takarar shugaban kasa, zan mayar da Borno kamar Jihar Kano.
"Wannan ziyarar ya nuna min cewa Allah ya kawo canjin da aka bukata; dandazon mutanen da suka tarbe mu tun daga filin jirgin sama zuwa cikin gari alama ce karara da ke nuna mutanen jihar Borno sun gaji kuma suna son canji a siyasar jihar.
"Wadanda suka kawo muku koma baya suna nan har yanzu suna son a cigaba da harka yadda suka saba inda wasu tsiraru kawai ke amfana; muna son canja hakan ta yadda kowane dan jiha zai amfana."

Kara karanta wannan

Ai Tuni Kwankwaso Ya Gaje Farin Jini da Kuri'un Buhari milyan 12 a Arewa, AbdulMumini Jibrin

Kwankwaso ya ce yana son kawo zaman lafiya mai dorewa a jihar ta yadda dukkan yan gudun hijira za su koma gidajensu a bude makarantu da asibitoci da sauransu, rahoton Information Nigeria.

Tsohon gwamnan na Jihar Kano ya shawarci magoya bayan jam'iyyar su yi koyi da abin da ake yi a Kano - jefa kuri'u da kuma kare kuri'un.

Ya kara da cewa:

"Abin da muke yi a Kano shine duk wani mai zabe wakilin jam'iyya ne kuma za mu tabbatar an kirga kuri'arku an kuma kare ta. Da irin yawan mutanen da na gani da ido na, wadanda suka tarbe mu daga filin jirgin sama zuwa sakatariya, na tabbatar NNPP za ta ci zabe 100 bisa 100 a Jihar Borno."

Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Rufe Ofishin NNPP Da Yan Sanda Suka Yi A Borno Gabanin Ziyararsa

A wani rahoton, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shuganan kasa na jam'iyyar New Nigeria People Party, NNPP, da jami'an tsaro suka yi a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An Bude Sakatariyar NNPP A Jihar Borno, Zulum Ya Bamu Hakuri: Kakakin Kwankwaso

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, tsohon gwamnan na Jihar Kano ya yi Allah-wadai da matakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164