Obasanjo Ya Gana da Tsofaffin Shugaban Ƙasa Biyu A Neja, Ya Fadi Matsayarsa a 2023

Obasanjo Ya Gana da Tsofaffin Shugaban Ƙasa Biyu A Neja, Ya Fadi Matsayarsa a 2023

  • Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ziyarci IBB da Janar Abdulsalmi Abubakar a Minna, jihar Neja ranar Lahadi
  • Obasanjo ya bayyana cewa ba shi da wani ɗan takarar shugaban ƙasa da yake goyon baya, ajendar ƙasa ya sa a gaba
  • A ƴan makonnin nan, Obasanjo ya gana da yan takarar jam'iyyu da wasu fitattun yan siyasa a Najeriya

Niger - Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa ƙawancen da ya kulla da wasu yan takarar shugaban ƙasa ba yana nuna alamun yana da zaɓin ɗan takarar bane, kishin ƙasa ya sa a gaba.

Vanguard ta ruwaito Dattijon ƙasan na cewa ba shi da wani ɗan takara da ya ke goyon bayan ko wata jam'iyya da yake so, amma ya sa kishin ƙasa a gaban komai.

Kara karanta wannan

Hotuna: Tinubu, Shettima, Adamu da Jiga-Jigan APC Sun Sa Labule a Abuja bayan Ganawa da Wike

Obasanjo ya yi wannan furucin ne a Minna, babban birnin jihar Neja bayan ya sa labule a lokuta daban-daban da tsoffin shugabannin ƙasa a mulkin soja, Janar Badamasi Babangida da Abdulsalami Abubakar ranar Lahadi.

Obasanjo da Abdulsalami.
Obasanjo Ya Gana da Tsofaffin Shugaban Ƙasa Biyu A Neja, Ya Fadi Matsayarsa a 2023 Hoto: Punchng/facebook
Asali: Facebook

"Bani da wani ɗan takara na musamman a zaɓen shugaban kasa na 2023, amma ina da kishin ƙasa, ina da Ajenda ta ƙasa," Inji Obasanjo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a ƴan kwanakin nan, an ga Obasanjo ya gana da yan takarar shugaban kasa na jam'iyyu daban-daban kuma a lokuta mabanbanta.

Tsohon shugaban ƙasa na tsawon zango biyu ya sa labule da Peter Obi na Labour Party, Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC da wasu fitattun ƴan siyasa a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Obasanjo, wanda ya isa a bakar Mota Jeep da misalin ƙarfe 12:30 na rana ya nufi gidan Janar Abdulsalami kai tsaye, inda suka shafe kusan mintuna 30 suna ganawar sirri.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar Ya Sa Labule da Gwamna Wike da Wasu Gwamnoni Uku a Landan

Me Ya kai Obasanjo wurin Abdulsalami?

Da yake amsa tambayoyin yan jarida bayan ganawarsa da Abdulsalami, tsohon shugaban ya ce ya zo ne domin ya ziyarci "Ɗan uwansa."

"Na zo ne na ga ɗan uwana wanda ke halin rashin lafiya kuma tun lokacin da yake kasar waje na so kai masa ziyara amma Allah bai nufa ba saboda ranar da na isa Landan kai masa ziyara a ranar ya baro ƙasar."
"Tun wannan lokacin da ban samu ganinsa ba a Landan, na kudiri zuwa na gaishe shi a Najeriya kuma wannan ne maƙasudin zuwa na. Shi mutum ne na musamman kuma ba shi da lafiya shiyasa na zo."

Obasanjo Ya ziyarci IBB

Janar Abdulsalami da matarsa mai shari'a Fati Abubakar, sun rako tsohon shugaban har gaban Motarsa bayan kammala ganawar su da karfe 1:13 na rana.

Daga nan, Obasanjo ya tafi zuwa gidan Janar Ibrahim Badamasi Babangida, inda anan ma suka gana da juna a sirrance.

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala a PDP, Ɗan Takarar Gwamna Ya Fice, Ya Koma Bayan Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

A wani labarin kuma Jiga-Jigan APC da Mambobi Sama da 19,000 Sun Koma PDP a Shiyyar Shugaba Buhari

Mambobi haɗi da shugabannin APC 19,500 sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP a mazaɓar Sanata mai wakiltar shiyyar Daura.

Shugaban PDP a Jihar Katsina, Hon. Salisu Yusuf Majigiri, ya ce masu sauya shekan sun fito ne daga ƙananan hukumomi biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel