2023: Jam'iyyar PDP Ta Karbi Mambobin APC Sama da 19,000 a Shiyyar Buhari

2023: Jam'iyyar PDP Ta Karbi Mambobin APC Sama da 19,000 a Shiyyar Buhari

  • Mambobi haɗi da shugabannin APC 19,500 sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP a mazaɓar Sanata mai wakiltar shiyyar Daura
  • Shugaban PDP a Jihar Katsina, Hon. Salisu Yusuf Majigiri, ya ce masu sauya shekan sun fito ne daga ƙananan hukumomi biyu
  • Yakubu Lado Ɗanmarke, mai neman gwamnan Katsina ya ce da zaraan ya ci zaɓe zai magance damuwar mutanen Katsina

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Mambobin jam'iyyar APC masu rijista 19,500 sun sauya sheka zuwa PDP a shiyyar Daura, yankin da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya fito a jihar Katsina.

Jaridar This Day ta rahoto masu sauya shekan na cewa gaza cika alƙawurran da gwamnatin APC ta ɗauka, matsin tattalin arziki da kalubalen tsaron da ya addabi jihar ne ya sa suka ɗauki wannan matakin.

Sauya Sheka a shiyyar Daura.
2023: Jam'iyyar PDP Ta Karbi Mambobin APC Sama da 19,000 a Shiyyar Buhari Hoto: Suleiman Abdullahi Dabai/facebook
Asali: Facebook

Da yake karɓan masu sauya sheƙan a garin Ɓaure ranar Asabar, shugaban PDP na Katsina, Hon. Salisu Yusuf Majigiri, ya ce masu sauya sheƙan 19,500 sun fito ne daga ƙananan hukumomin Ɓaure da Zango.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hukumar DSS Ta Saki Fitacciyar Mai Goyon Bayan Ƙungiyar 'Yan Ta'adda a Najeriya

Kananan hukumomin biyu na cikin guda 12 da suka haɗu suka yi mazaɓar Sanatan shiyyar Daura, inda shugaban kasa Buhari ya fito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar shugaban PDP:

"Yau mun karɓi mambobi 19,500 da suka sauya sheka daga APC zuwa PDP kuma mafi yawan su shugabanni ne a tsohuwar jam'iyyarsu daga gundumomi daban-daban na Ɓaure da Zango, zami aiki tare wajen ceto Katsina a 2023."

Ya nemi kafatanin masu sauya shekan su koma yankunan su kana su yi aiki tukuru domin jam'iyyar PDP ta kai ga gaci, inda ya ƙara da cewa jam'iyyar ta shirya kwace mulki daga hannun APC.

Dan takarar PDP a Katsina, Ɗanmarke da Sanata Babba Kaita.
2023: Jam'iyyar PDP Ta Karbi Mambobin APC Sama da 19,000 a Shiyyar Buhari Hoto: Suleiman Abdullahi Dabai/facebook
Asali: Facebook

Ku shirya yaƙin kwato Katsina - Lado

Tun da farko ɗan takarar gwamnan Katsina a Inuwar PDP, Yakubu Lado Ɗanmarke ya yi kira ga masu sauya shekan su tashi tsaye su shirya kan su kuma su yi fatali da duk wata yaudara da za'a ɓullo musu da ita a yaƙin nasara a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Daga Karshe, Shekarau Ya Yanke Jam'iyyar Da Zai Koma Bayan Ganawa da Atiku da Tinubu

Ya ƙara da bayanin cewa PDP ta jima tana karban masu sauya sheka daga sauran jam'iyyun siyasa a jihar. Ya yi hasashen cewa kafin ranar zaɓe PDP ka iya karɓan mutum 100,000.

Ɗanmarke ya kara da cewa idan ya ɗare kujerar gwamna, gwamnatinsa zata fatattaki talauci, ta magance taɓarɓarewar tattalin arziki da kalubalen tsaro da ya damu jihar.

A wani labarin kuma Ɗan Takarar Gwamna A PDP Ya Fice Daga Jam'iyyar, Ya Samu Tikitin Takara a 2023

Wani da ya nemi tikitin takarar gwamnan Ogun a inuwar PDP ya nuna fushinsa a fili, ya sauya sheƙa zuwa PRP.

Farfesa Olufemi Bamgbose, ya samu tikitin takarar gwamna a sabuwar jam'iyyarsa da zai ba shi damar shiga zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel