Gwamnan Bauchi Ya Watsar Da Mataimakinsa, Ya Dauki Sabon Abokin Takara a 2023

Gwamnan Bauchi Ya Watsar Da Mataimakinsa, Ya Dauki Sabon Abokin Takara a 2023

  • Gwamnan Bauchi ya aje mataimakinsa na yanzu, ya zaɓi ɗan majalisar tarayya a matsayin abokin takararsa na zaɓen 2023
  • Hon. Mohammed Auwal Jatau, ya yaba wa gwamnan bisa wannan girma da ya ba shi, ya yi alƙawarin ba zai ba shi kunya ba
  • Ya tabbatar wa mazauna jihar Bauchi cewa, Gwamna Bala Muhammed, ya shirya ninka ayyukan da zai musu a zango na biyu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi kuma ɗan takarar gwamna a PDP, Bala Muhammed, ya ayyana mamban majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Zaki, Hon. Mohammed Auwal Jatau, a matsayin abokin takararsa na zaɓen 2023.

Honorabul Jatau ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa ɗa ƴan jarida ranar Lahadi a Bauchi, babban burnin jihar ta Bauchi.

Gwamnan Bauchi, Bala Muhammed.
Gwamnan Bauchi Ya Watsar Da Mataimakinsa, Ya Dauki Sabon Abokin Takara a 2023 Hoto: @Senbalamohammed
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa mataimakin gwamnan mai ci, Baba Kaka Tela, ya rasa damar neman tazarce tare da gwamna Muhammed a babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Kara karanta wannan

"An Cuce Ni" Ɗan Takarar Gwamna A PDP Ya Fice Daga Jam'iyyar, Ya Samu Tikitin Takara a 2023

Sabon ɗan takarar mataimakin gwamna ya gode wa mai girma Gwamna Bala Muhammed bisa ganin ya dace da zaɓo shi a matsayin abokin takara a zaɓen 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma tabbatar da cewa zai nuna shi ɗan halak ne kan wannan alfarma ta hanyar zama mataimakin gwamna mai biyayya da goyon baya domin nasarar gwamnatin PDP mai ci a Bauchi.

A jawabinsa, ɗan majalisar ya ce:

"Wannan ba karamar girmama wa bace a gare ni kuma ina mai tabbatar wa gwamna cewa ba zan ba shi kunya kan yakinin da yake da shi a kaina bs. Ba gwamnatin da ta kyautata kamar ta Ƙauran Bauchi."
"Baki ɗayan mu mun yi mamakin aikin da gwamna ya aiwatar ta yadda mazauna suka dangwali romon demokaraɗiyya babu nuna banbanci, ya zama dole a gare mu, mu tafa wa mai girma gwamna don ya sa mu alfahari."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Allah Ya Yiwa Sarkin Funukaye, Alhaji Muhammad Muazu Kwaranga, rasuwa

"Kanfen da zamu yi na 2023 zai dogara ne kacokan kan nasarorin da muka samu da waɗan da zamu yi a zango na biyu kuma Insha Allah ayyukan gwamna zasu taka rawa wajen nasarar mu."

Zamu yi abinda ya zarce na farko - Jatau

Ɗan majalisar ya kara tabbatarwa mutane Bauchi cewa ayyukan da gwamna ke da kudirin yi a zango na buyu zai zarce dumbin ayyukan da suka shaida a zangon farko.

A wani labarin kuma Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Magantu Kan Yuwuwar Haɗa Kai Da Wata Jam'iyya a 2023

Ɗan takarar shugaban ƙasa karƙashin inuwar SDP ya ce jam'iyyarsa ba zata yi haɗin guiwa da kowace jam'iyya ba a zaɓen 2023.

Prince Adewole Adebayo, da ke fatan ɗare wa kujerar Buhari a 2023 ya ce duk da ana gani ba su tabuka komai ba zasu shiga zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262