Kotu Ta Soke Zaɓen Kananan Hukumomin Jihar Ebonyi Wanda APC Ta Lashe
- Babbar Kotun tarayya da ke zama a Abakaliki ta soke zaɓen kananan hukumomin jihar Ebonyi wanda aka gudanar ranar 30 ga watan Yuli
- Alkalin Kotun, Mai shari'a Rilman Fatun, ya ce zaben ya saba wa tanadin sabon kundin zaɓen 2022
- Jam'iyyar PDP ta kalubalanci sakamakon zaɓen a Kotu, inda ta yi zargin hukumar zaɓe da gwamnatin jihar sun karya doka
Ebonyi - A yau Alhamis, Babbar Kotun tarayya da ke zamanta a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi ta soke zaɓen kananan hukumomin da aka gudanar a faɗin jihar.
A cewar Kotun, zaɓen kananan hukumomin da ya gudana ranar 30 ga watan Yuli, 2022, ya saɓa wa tanadin sabon kundin dokokin zaɓen 2022, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Jam'iyyar PDP ta ƙalubalanci sakamakon zaɓen, inda ta zargi hukumar zaɓe da gwamnatin jihar Ebonyi ta yi sashi na 150 na kundin dokokin zaɓe 2022 hawan ƙawara da sauran hujjoji.
Alƙalin Kotun Mai shari'a Justice Rilman Fatun, a ƙara mai lamba FHC/AI/CS/151/2022, ya yanke hukuncin cewa zaɓen ya saɓa wa tsarin demokaraɗiyya da tanadin doka a sirrance.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan cigaban na zuwa kwanaki shida kacal gabanin rantsar da sabbin zaɓaɓɓun shugabannin kananan hukumomi da Kansiloli, wanda aka shirya gudanarwa ranar 1 ga watan Satumba.
Kotu ta yi adalci - PDP
Da yake jawabi jim kaɗan bayan hukuncin Kotu, Lauyan PDP, Mudi Erhenedi, ya jinjina wa Kotun bisa tabbatar da adalci a jihar, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Erhenedi ya ƙara da cewa masu shigar da ƙara sun rubuta takarda zuwa hukumomin da ke da alhaki da lamarin, ciki har da majalisar dokokin jihar Ebonyi, an faɗa musu matsalolin da ke tattare da gudanar da zaɓen.
Roy Nweze, lauyan da ke kare waɗan da ake ƙara, bai ɗaga kiran da akai ta jera masa ba domin ya yi ƙarin haske kan hukuncin da Kotu ta yanke.
A wani labarin kuma Atiku Abubakar Ya Gana Da Gwamna Wike da Wasu Gwamnoni Uku a Landan
Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gana da gwamna Wike na jihar Ribas a birnin Landan.
Rahoto ya nuna cewa taron ya samu halartar gwamnonin PDP uku daga tsagin Wike yayin da Gwamnan Adamawa ke tare da Atiku.
Asali: Legit.ng