Kada Ku Kuskura Ku Zabi Shugabannin da Ba Su Cancanta Ba, Shawarin Sarki Sanusi Ga ’Yan Najeriya
- Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ba 'yan Najeriya shawari kan wanda ya kamata su zaba a 2023
- Sanusi ya yi tsokaci game da halin da Najeriya ke ciki, da kuma wuraren da ya kamata a mayar da hankali sosai
- Ana ci gaba da shirin zaben 2023, 'yan Najeriya da dama na bayyana irin shugabannin da ya kamata a zaba
Jihar Legas - Sarkin Kano na 14, kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya ba 'yan Najeriya shawarin irin shugabannin da ya kamata su zaba a zaben 2023 mai zuwa.
Muhammadu Sanu II, ya ce ya kamata 'yan Najeriya natsu su zabi shugabannin da ke da kwarewa ta gudanar da kasa a zabe mai zuwa, kuma su kauda batun kabilanci, TheCable ta ruwaito.
Sanusi ya bayyana hakan ne a jiya Laraba 24 ga watan Agusta a jihar Legas taron The August Event 2022 da gidauniyar Moses Adekoyejo Majekodunmi tare da hadin gwiwar Asibitocin Santa Nicholas suka shirya.
Sanusi ya bayyana cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Ya kamata a titsiye 'yan siyasa domin su fadi shirinsu kan asibitoci da ilimi da sauran muhimman bangarorin da suke da koma baya a kasar nan.
“Gwamnati dai ta daina mutunta wannan sana’ar kuma babu adadin kudaden da za a kashe a fannin ilimi ta albashi a kasar nan da zai kawo sauyi. Likitoci da malamai ya kamata gansu cikin rayuwa mai kyau da mutuntawa."
Ya kuma bayyana cewa, bangare mafi kyau da zai gyara kowace kasa a duniya shi ne ilimi, inda ya koka da cewa, akwai bukatar martaba ilimi da kiwon lafiya a Najeriya.
Game da tattalin arziki
Da yake magana kan yadda Najeriya ke cikin matsin tattalin arziki, Sanusi ya tuna da yadda Najeriya take a baya da kuma a yanzu, rahoton kafar labarai ta Reuben Abati.
Ya ce:
“A 2016, an ga hauhawar farashin kayayyaki zuwa 18%, lamarin da ya sa farashin komai ya ninka akalla sau biyu duk bayan shekaru hudu. Buhun shinkafa da aka ana sayar dashi Naira 8,000 a 2015, yanzu kuma ya kai N35,000.
Ya kuma tuna yadda a shekarar 2011 aka kai ruwa rana game da tallafin man fetur, inda yace gashi a yanzu gwamnatin Buhari na duba kashe akalla N6.7tr da sunan kudin tallafin mai.
Tsohon Sarkin Kano Sanusi Ya Bukaci Matasa Su Daina Fita Waje, Su Tsaya a Najeriya
A wani labarin, tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na biyu, ya yi kira ga matasan Najeriya da su daina barin kasar nan domin neman dama a kasashen waje, rahoton TheCable.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Sanusi ya yi wannan kira ne ga matasan yayin da yake jawabi a ranar Lahadi a wani wasan kwaikwayo mai taken 'A Truth in Time.
Taron wanda ya naqalto rayuwa da gogewar tsohon sarkin, Ahmed Yerima, farfesa ne na fannin wasan kwaikwayo a Jami’ar Redeemer, ya rubuta shi, wanda Duke of Shomolu Productions ya shirya.
Asali: Legit.ng