2023: NNPP Ba Za Ta Ruguza Tsarinta Ba Saboda Kwankwaso Ya Hade da Tinubu, Inji Farfesa Alkali

2023: NNPP Ba Za Ta Ruguza Tsarinta Ba Saboda Kwankwaso Ya Hade da Tinubu, Inji Farfesa Alkali

  • Shugaban jam'iyyar NNPP na kasa, Farfesa Rufa'i Alkali ya bayyana matsayar jam'iyyar kan maja tsakanin Kwankwaso da Tinubu
  • Ana yada rade-radin cewa, akwai yiwuwar Kwankwaso ya marawa Tinubu baya a zaben 2023 mai zuwa
  • A baya an samu cece-kuce yayin da jigon NNPP a Kano, Mallam Ibrahim Shekarau ya sauya sheka a makon nan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Legas - Jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari ta musanta yunkurin ruguza tsarinta domin hada kai da sauran jam'iyyun siyasa, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban jam’iyyar na kasa Farfesa Rufa’i Alkali, ya ce sam jam'iyyar ba ta da shirin sayar da kimarta a matsayinta na jam'iyya mai rajista ga kowace jam'iyya a kasar nan.

Alkali ya yi wannan tsokaci ne a jihar Legas yayin da yake yiwa manema labarai karin haske game da matsayar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPP Alkali: Kar a sako jam'iyyar NNPP a rikicin Shekarau da Kwankwaso

Kwankwaso ba zai hade da Tinubu ba, inji shugaban NNPP
2023: NNPP Ba Za Ta Ruguza Tsarinta Ba Saboda Kwankwaso Ya Hade da Tinubu, Inji Farfesa Alkali | Hoto: kemifilani.ng
Asali: UGC

Ya musanta batutuwan da ke yawo cewa, dan takararsu, Rabiu Musa Kwankwaso da magoya bayansa na tattauna yadda za su hada kai da Tinubu, ICIR ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce, maganar maja ta wuce a yanzu, kamar yadda dokoki da ka'idojin hukumar zabe mai zaman kanta suka tanada.

Batun ficewar Shekarau daga NNPP

Da yake magana game da batun ficewar Sanata Ibrahim Shekarau daga cikinsu, ya ce wannan batu ne na radin kai, kuma bai kamata jam'iyyar NNPP ta zama maudu'in tattauna game da shawarin Shekarau ba.

A bangare guda, ya ce jam'iyyar na martaba Shekarau, don haka ta goyi bayan hukuncin da ya yanke na ficewa daga cikinta.

Hakazalika, ya ce a halin yanzu dai ana ci gaba da tattauna da Shekarau don warware zaren rikicin da ke tsakaninsa da wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin PDP, Na Hannun Daman Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC

Kwankwaso Masoyin Inyamurai Ne, Inji Wanda Ya Assasa Jam’iyyar NNPP

A wani labarin, ma'assasin jam'iyyar NNPP Boniface Aniebonam ya ce jam'iyyar bata yi zaben tumun dare ba da ta zabi Rabiu Kwankwaso a matsayin dan takarar shugaban kasanta a 2023.

Ya kuma bayyana cewa, Kwankwaso masoyi ne ga kabilar Igbo da duk al'ummar Kudu maso Gabashin Najeriya, Premium Times ta ruwaito.

Jagoran na NNPP ya bayyana hakan ne a yau Talata 23 ga watan Agusta a jihar Legas a wani taron da aka shirya na kaddamar da shirin NNPP karkashin Prime Maritime Project (PMP).

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.