2023: Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Jerin ‘Yan Takaran da Buhari Zai Marawa Baya
- Malam Garba Shehu yace akwai wasu ‘Yan takaran da Shugaba Muhammadu Buhari ba zai mara masu baya a zaben 2023 ba
- A wani jawabi da Garba Shehu ya fitar, yace babu ruwan Shugaban kasar da takaran wadanda suka fice daga jam’iyyar APC
- Sannan Shugaban Najeriyan ba zai taimaka wajen kamfe ga duk wani wanda ya shiga kotu da ‘dan takaran da APC ta tsaida ba
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sai ‘yan takaran da jam’iyyar APC ta tsaida kadai zai taya kamfe a zabe mai zuwa na 2023.
The Nation ta rahoto Garba Shehu yana cewa babu ruwan Mai girma Muhammadu Buhari da tsofaffin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da suka sauya-sheka.
Kamar yadda Malam Shehu ya fada a jawabin da ya fitar a ranar Laraba, shugaban kasar ba zai taya wadanda suka kai APC kotu wajen kamfe ba.
Hadimin shugaban kasar yace Mai gidansa ba zai ci amanar jam’iyyarsa ta APC a zaben badi ba.
“Fadar shugaban kasa tana so ta fayyace kuma ta tabbatarwa asalin ‘yan jam’iyyar APC cewa Muhammadu Buhari yana nan da tarbiyarsa ta sojan APC.
A duka zabe mai zuwa, zai mara baya ne kurum ga ‘yan takaran da jam’iyya ta tsaida, ba wasu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan jan-kunne ne ga wadanda suka shiga wata jam’iyya, da wadanda suka je kotu da ‘yan takaran da APC ta tsaida, wadannan za su karata can.”
- Garba Shehu
A jawabin, shugaban na Najeriya yace bai da alaka da wadanda suke shari’a da jam’iyyarsu, ya jaddada cewa zai maidawa APC alherin da ta yi masa a 2015.
Su wa wannan za ta shafa?
The Cable ta rahoto Shehu yana cewa jawabin shugaban kasar bai nuni ga wani ‘dan takaran 2023.
Amma Legit.ng Hausa ta fahimci wannan mataki da shugaban kasar ya dauka zai shafi wasu na kusa da shi, da yanzu sun tsallaka wata jam’iyyar siyasa.
Daga cikinsu akwai tsohon mai ba shi shawara wajen yada labarai, Hon. Sha’aban Sharada wanda yake takarar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar ADP.
Haka zalika akwai Abdulrahman Kawu Sumaila mai neman takarar Sanatan Kano ta Kudu a 2023. Bugu da kari, Hon. Fatuhu Muhammad da ya fice daga APC.
NNPP ta na shiga ko ina
An ji labari Farfesa Rufa’i Alkali ya bayyana cewa ba daidai ba ne a rika tunani NNPP ba ta da karfin da za ta iya lashe zaben shugabancin Najeriya a 2023.
Shugaban jam’iyyar ta NNPP ta kasa yace duk Najeriya, babu jam’iyya mai ratsa kasa sosai a yanzu irin NNPP da ake yi wa lakabi da mai kayan marmari.
Asali: Legit.ng