Bayan Samun Tikitin Jam’iyya, ‘Dan takaran APC zai Fuskanci Shari’a 19 Kafin 2023
- Ikechi Emenike ya bayyana irin kalubalen da yake fuskanta duk da tsaida shi a matsayin ‘dan takarar Gwamna a jihar Abia
- ‘Dan siyasan da zai rikewa jam’iyyar APC tuta a zaben shekara mai zuwa ta 2023 zai kashe tulin kudi wajen kare kan shi a kotu
- Kawo yanzu Emenike ya yi shari’a 13 da mutane a gaban Alkali, kuma har gobe akwai sauran zama kotu 6 da suke gabansa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abia - Ikechi Emenike wanda jam’iyyar APC ta ba takarar gwamna a jihar Abia, ya tabo batun tulin karan da aka kai shi a kotu bayan zaben gwani.
PM News tace Ikechi Emenike ya yi magana a garin Okoko Item a karamar hukumar Bende ta jihar Abia, wajen kaddamar da abokiyar takararsa a APC.
‘Dan takaran gwamnan ya zabi Gloria Akara ta zama mataimakiyarsa a zaben 2023. Akara ta shafe kusan shekaru 40 tana aikin kotu, sannan fasto ce.
Shekara da shekaru kenan Akara tana jagoranci a cocin God’s Heritage Ministry a Fatakwal.
An ci karfin shari'a 13
A Okoko ne ‘dan takaran yake bayani game da karar da aka kai shi a kotu. Emenike yake cewa ya yi nasarar fatali da shari’a 13, yanzu wasu shida na nan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
NNN tace ‘dan siyasar ya nuna yana sa ran za iyi galaba a sauran shari’o’in da za ayi da shi, yace yana fatan ya samu nasara kamar yadda ya dace a baya.
A kan dauko Gloria Akara takara kuwa, Emenike yace ya dauki wannan mataki a APC ne domin nuna da gaske suke yi wajen daidaita maza da mata.
Tun da Abia ta zama jiha a Najeriya a 1991, ba a taba daukar mace ta zama ‘yar takarar gwamna ba, sai wannan karo jam’iyyar ke neman kafa tarihi.
A ra’ayinsa, zaman mace mataimakiyar gwamna zai kawo karshen satar dukiyar al’umma.
Mutanen Awka sun samu takara
Rahoton yace ‘dan takaran mai fuskantar barazana iri-iri a kotu yace ya dauko abokiyar takararsa daga Awka ne domin an dade ba ayi da yankin.
Babban burin Emenike shi ne ya karbi gwamnati a Abia ta yadda zai daura tubalin kawowa jama’a cigaba, don haka ya yi kira ga duk 'Yan APC su mike.
Aisami: JIBWIS tayi Allah-wadai
Dazu aka ji labari Sheikh Abdullahi Bala Lau ya tabbatar da cewa Musulmai ba za su yarda da kisan da aka yi wa Sheikh Goni Aisami a jihar Yobe ba.
Bala Lau yana ganin da wani Musulmi ne ya kashe Fasto, to da wani labarin da dabam ake yi yanzu, don haka ba za su bari maganar ta lalace ba.
Asali: Legit.ng