Matasa Sun Lakadawa Wani Bishap Duka Bisa Zargin Ya Halarci Taron Kaddamar da Shettima

Matasa Sun Lakadawa Wani Bishap Duka Bisa Zargin Ya Halarci Taron Kaddamar da Shettima

  • Wasu fusattatun matasa sun farmaki wani Bishap da suka zarga da halartar taron APC a kwanakin baya
  • An yi ta cece-kuce a Najeriya yayin da Bola Ahmad Tinubu ya kaddamar da Kashim Shettima a matsayin abokin takara
  • Kungiyar CAN ta zargi fastocin bogi da shiga harkar siyasa, inda ta nisanta kanta da wasu da aka ce Bishap ne

FCT, Abuja - Wasu futattun matasa sun farmaki wani Bishap da suka yi zargin yana daya daga cikin fastocin bogi da suka halarci taron APC na kaddamar abokin takarar Tinubu; Kashim Shettima.

A wani faifan bidiyon da bazu a kafafen sada zumunta, an ga wasu matasa na cin zarafin wani mutumin da ke kama da Bishap din da aka gani a taron su Tinubu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karon Farko a Tarihi, Buhari Ya Kirkiro Sabon Mukami Domin Magance Rashin Tsaro

A cewar wani mai amfani da kafar Facebook, Sunday Wale Adeniran, mutumin da aka ce sunansa wai “Rev Chika” dan kabilar Agulu ne a jihar Anambra, Kudu maso Gabashin Najeriya.

Matasa sun yi aika-aika, sun lakadawa wani fasto duka
Matasa sun lakadawa wani Bishap duka bisa zargin ya halarci taron kaddamar da Shettima | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A rubutun da ya yada, Adeniran ya bayyana cewa, an yiwa wannan Bishap rashin mutunci ne a yankin Dei-dei ta babban birnin tarayya Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani bidiyon da wakilinmu ya gani a shafin Twitter na Henry Shield ya nuna lokacin da matasan ke aika-aikan.

Martanin 'yan sanda

Da aka nemi jin ta bakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja, mai magana da yawun rundunar, DSP Josephine Adeh, ta ce bata san komai game da lamarin ba.

Sai dai, ta bayyana ci gaba da kafin daga bisani ta tuntubi manema labarai game da lamarin.

A tun farko, 'yan Najeriya da dama, musamman kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ta nuna kin amincewarta da zabo Musulmi a matsayin abokin takarar Tinubu.

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Kotu ta yankewa kasurgumin dan bindiga hukuncin zaman gidan magarkama

Wannan lamari ya yi kamari, har ta kai kungiyar ta ce lallai fastocin da suka halarci taron kaddamar da Shettima na bogi ne.

Amma, Bayo Onanuga, daraktan harkokin sadarwa na gangamin Tinubu ya dage cewa fastocin na gaske ne, kuma su suka yi radin kansu suka zo.

Tinubu da Shettima: CAN ta yi bore da martani mai zafi kan tikitin Muslmi da Musulmi

A wani labarin, kungiyar kiristocin Najeriya CAN ta ki amincewa da zabo tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Da yake magana a wata hira da jaridar Punch a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, mai magana da yawun CAN, Adebayo Oladeji, ya ce yanke irin wannan shawari a cikin kasa mai cike da rudani irin Najeriya, mataki ne da bai dace ba.

Ya bayyana cewa, kasar na da fasto a matsayin mataimakin shugaban kasar kuma ake kashe malamai da mabiya addinin kirista, to lallai babu tabbacin kiristoci za su samu aminci a mulkin Musulmi da Musulmi.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Matashin da ya durawa kabarin mahaifiyar abokinsa ashariya ya shiga hannu

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.