Ana Za a Bar Mulki, Tsohon ‘Dan Majalisa yace Ganduje Bai Ci Zaben 2019 ba

Ana Za a Bar Mulki, Tsohon ‘Dan Majalisa yace Ganduje Bai Ci Zaben 2019 ba

  • Hon. Abdulmumin Jibrin yana da ra’ayin cewa Abdullahi Umar Ganduje bai yi nasara a zaben Gwamnan jihar Kano a 2019 ba
  • Tsohon ‘dan majalisar yace Rabiu Kwankwaso da mutanensa a PDP suka lashe zaben Gwamna, amma a karshe APC ta zarce
  • Kan batun Ibrahim Shekarau, jagoran na NNPP ya yau ya ce tun zaben 2015, Kwankwaso ne yake yin galaba a siyasar Kano

Abuja - Abdulmumin Jibrin ya yi hirar farko da gidan talabijin Channels TV bayan zamansa mai magana da yawun yakin neman shugaban kasar NNPP.

A tattaunawar da aka yi da Hon. Abdulmumin Jibrin a ranar Alhamis, 18 ga watan Agusta 2022, ya tabo batutuwan da suka shafi gwamnati da siyasar kasa.

Da yake amsa tambaya a game da makomar Sanata Ibrahim Shekarau a NNPP, Jibrin ya nuna ko Sanatan ya sauya-sheka, jam’iyyarsu za ta kai labari a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Yadda Gwamnonin PDP da Jiga-jigan Jam’iyya Suka Yi Watsi da Atiku a Yola

Wani gutsuren bidiyon hirar da ya shigo hannun Legit.ng ya nuna kakakin kwamitin neman takarar na NNPP yana cewa babu wani wanda zai iya kada NNPP.

Kwankwaso ya rike siyasar Kano

Tsohon ‘dan majalisar yace a 2019 an ga aya a zaben Kano, inda duk manyan ‘yan siyasa suka tare a APC, amma Rabiu Kwankwaso ya nuna masu nauyinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jibrin yana jam’iyyar APC a lokacin zaben 2019, yayin da Kwankwaso da mutanensa su na PDP. ‘Dan siyasar ya dauko tarihin siyasar jihar Kano tun daga 2015.

Kwankwasiyya
Kwankwaso da Jagororin NNPP a Kano Hoto: Saifullah Hassan
Asali: Facebook

Taron dangin APC bai yi aiki ba

“A 2019, abin takaici, dukkaninmu sai mu ka bi Ganduje, Shekarau, Kabiru Gaya, Barau Jibrin, Kawu Sumaila, duk wani babba a Kano ya bi Ganduje,
Meya faru? Kwankwaso shi kadai a gefe guda, ya doke mu a zaben Gwamna. Abin da ya faru a zaben, abin da aka gani ne, amma a gaskiya ya ci zabe

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya yi Nadin Mukamai a Shirin Takarar Shugaban kasa a NNPP

Saboda haka idan ana zawarcin Shekarau, me ake nama ne, na gagara fahimtar wannan. Babu wanda zai bar NNPP a Kano da zai jijjiga Kwankwaso.”

A karshen wannan gabar, Jibrin wanda ya wakilci Kiru da Bebeji a majalisar tarayya yace hakan bai nufin yana kokarin cin mutuncin tsohon Gwamna Shekarau.

Hakan martani ga rade-radin da ake yi na cewa Malam Shekarau yana neman barin NNPP, yayin da wasu ke zargin ya sa labule da sauran ‘yan takaran 2023.

Shekarau zai fice daga NNPP?

A tsakiyar makon nan, mun samu labari Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ce tsakaninsa da mutanen Ibrahim Shekarau babu wata rigima kamar yadda ake fada.

‘Dan takaran shugaban kasar na NNPP ya shaidawa ‘yan jarida wannan, kuma ya fadi abin da ya sa ba su iya biyawa tsagin Shekarau bukatunsu a NNPP ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng