2023: Dalilin Da Yasa Ba Zamu Iya Cika Wa Shekarau Bukatunsa Ba, Kwankwaso

2023: Dalilin Da Yasa Ba Zamu Iya Cika Wa Shekarau Bukatunsa Ba, Kwankwaso

  • Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP ya ce ba zasu iya cika wa bangaren Shekarau bukata ɗaya ba
  • A cewar jagoran NNPP, jam'iyyar ta cika dukkan alƙawarin da ta ɗaukar wa Shekarau, banda na baiwa mutanensa takara
  • Wannan na zuwa ne a lokacin da ake yaɗa cewa Shekarau na shirin tattara komatsansa ya bar NNPP

Kano - Ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP mai kayan daɗi, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi bayanin dalilin da yasa jam'iyya ba zata iya cika ɗaya daga cikin bukatun tsagin Shekarau ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa Kwankwaso ya musanta raɗe-raɗin da yawo cewa basu ga maciji tsakanin shi da Malam Ibrahim Shekarau, sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya.

Rabiu Musa Kwankwaso da Ibrahim Shekarau.
2023: Dalilin Da Yasa Ba Zamu Iya Cika Wa Shekarau Bukatunsa Ba, Kwankwaso Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A wata hira da BBC Hausa, Kwankwaso ya ce jita-jitar da mutane ke yaɗa wa cewa suna takun saƙa tsakanin su ƙanzon kurege ne, inda ya kara da cewa ba wani abu makamancin haka a NNPP.

Kara karanta wannan

Zamu Ganar da Yan Najeriya, Basu da Zaɓin da Wuce Tinubu da Shettima a 2023, Adamu

Ya yi wannan furucin ne domin martani kan labarin dake cewa tsohon gwamnan Kano (Shekarau) ka iya tattara kayansa ya koma PDP saboda rashin cika alƙawarin da aka ɗaukar masa gabanin ya shiga NNPP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwankwaso ya ce:

"Babu alƙawarin da bamu cika ba in banda na yan takara, mun yi iya bakin kokarin mu don cika yarjejeniyar amma lokaci ya mana katsa landan."

Meyasa NNPP ta gaza cika masa alƙawarin takara?

A cewar Kwankwaso, mafi yawan mutanen da Shekarau ya bayar a basu tikicin takara, sun shigo NNPP ne a lokacin hukumar zaɓe INEC ta rufe karɓan yan takara.

Sai dai, Ɗan takarar shugaban ƙasan ya ce idan jam'iyyar ta lashe zaɓe kuma ta kafa gwamnati, zata ɗebo mutandn Shekarau ta basu manyan muƙamai.

Sanata Kwankwaso ya ƙara da cewa wannan ba zai kawo wani tarnaƙi a jam'iyyar NNPP ba, inda ya tabbatar da cewa babu wata matsala tsakanin shi da tsagin Shekarau.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wani Ɗan Jam'iyyar APC Ya Bindige Mutum Hudu a Babban Shagon 'Supermarket'

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Zai Tafi Maiduguri, Zai Kaddamar da Ayyukan Zulum da Tallafa Wa Talakawa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai bar fadarsa dake Abuja zuwa Maiduguri, jihar Borno domin ziyarar aiki a gobe Alhamis.

Wannan ziyarar da shugaban zai kai babban birnin jihar Borno ita ce ta uku cikin shekara ɗaya da ta gaba ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel