Shugaba Buhari Zai Kara Kai Ziyarar Aiki Maiduguri a Karo Na Uku

Shugaba Buhari Zai Kara Kai Ziyarar Aiki Maiduguri a Karo Na Uku

  • Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai bar fadarsa dake Abuja zuwa Maiduguri, jihar Borno domin ziyarar aiki a gobe Alhamis
  • Wannan ziyarar da shugaban zai kai babban birnin jihar Borno ita ce ta uku cikin shekara ɗaya da ta gaba ta
  • Buhari zai kaddamar da fara baiwa talakawa masu karamin ƙarfi tallafi da wasu ayyukan gwamnatin Zulum

Abuja - An kammala duk wasu shirye-shirye da ya kamata domin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai fara ziyarar aiki a birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Shugaban ƙasan zai tafi birnin Maiduguri ne ranar Alhamis, 18 ga watan Agusta, 2022, kamar yadda rahoton jaridar 21 Century ya tabbatar.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Shugaba Buhari Zai Kara Kai Ziyarar Aiki Maiduguri a Karo Na Uku Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: UGC

Wannan ziyarar da Buhari zai sake kai wa ita ce ta uku cikin shekara ɗaya bayan wacce ya kai jihar a ranar 17 ga watan Yuni da kuma ta ranar 23 ga watan Disamba duk a shekarar 2021.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Ƙasa Buhari Ya Dira Babban Birnin Jihar Borno, Hotuna Sun Bayyana

Daily Nigerian ta rahoto cewa yayin wannan ziyarar ta gobe, ana tsammanin Buhari zai kaddamar da fara ba da tallafin jin ƙai ga mutane marasa ƙarfi a jihar Borno.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka zalika, ana sa ran shugaban ƙasan zai kaddamar da Gidajen Malamai a gundumar Bukumkutu da wasu gidajen 500 da za'a sake maida yan gudun hijira a Molai.

Gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin gwamna Farfesa Babagana Umaru Zulum ce ta samar da baki ɗaya waɗannan ayyukan da ake sa ran shugaba Buhari zai kaddamar.

Bayan haka, Shugaban Ƙasan zai kai ziyarar gaisuwa ga iyayen ƙasa, fadar mai martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar el-Kanemi.

Saboda haka aka shawarci ɗaukacin al'umma musamman masu shirin yin tafiya da su fita tun safe domin guje wa cunkuson ababen hawa da ka iya tashe hanyoyi.

Kwankwaso ne zai gaji Buhari - Galadima

Kara karanta wannan

Yajin Aikin Ma'aikatan Wutar Lantarki: NUEE ta Garkame Ofishin TCN na Kaduna

A wani labarin kuma Buba Galadima ya yi ikirarin cewa Rabiu Kwankwaso ne zai lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023

Jigo a jam’iyya mai kayan marmari NNPP, Buba Galadima, ya yi ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso, ne zai gaji shugaban kasa, Muhammadu Buhari a 2023.

Daily Trust ta rahoto Galadima na cewa Kwankwaso zai yi nasara a baki ɗaya jihohin arewa maso yamma kana ya samu kuri’u isassu a sauran shiyyoyin Najeriya a zaben shugaban kasa da ke tafe a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel