Rigimar Gidan PDP Ta Cabe da Fitowar Tsohon Bidiyon Shugaban Jam’iyya

Rigimar Gidan PDP Ta Cabe da Fitowar Tsohon Bidiyon Shugaban Jam’iyya

  • Bode George yana nan a kan bakarsa, yace ya wajaba Iyorchia Ayu ya sauka daga shugabancin PDP
  • Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar adawar yana ganin ba ayi wa kudancin Najeriya adalci ba
  • Tun da Atiku Abubakar ya samu tuta a PDP, George yace akwai bukatar a tunawa Ayu kalamansa na 2021

Lagos – Daily Trust tace tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP, Olabode George ya dage cewa dole Iyorchia Ayu ya sauka daga kujerar shugaban PDP.

A ranar Talata, 16 ga watan Agusta 2022 aka ji Cif Olabode George yana cewa akwai bukatar Dr Iyorchia Ayu ya yi murabus saboda jam’iyya ta zauna lafiya.

George ya tunawa Duniya cewa Ayu ya yi alkawarin zai sauka daga kan kujerarsa da zarar ‘dan siyasar Arewa ya samu takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku da Wike: Daga Karshe, Shugaban PDP Ya Magantu Kan Bukatar Ya Yi Murabus

Jaridar tace George ya kalubalanci shugaban na PDP ya rubuta takardar murabus tun da Atiku Abubakar aka tsaida takarar shugaban Najeriya a inuwar PDP.

An maida 'Yan Kudu saniyar ware

Tsohon ‘dan siyasar ya sanar da Atiku Abubakar cewa ‘Yan PDP a Kudancin Najeriya ba su bukatar kujerar Darekta Janar na yakin zaben shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda aka fitar da rahoto, Bode George yace da ‘Yan Arewa ne a rigar mutanen Kudu, sam ba za su yarda wani yanki ya tattara mukamai a haka ba.

Iyorchia Ayu
Shugaban Jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

Iyorchia Ayu yace shekara hudu zai yi ofis a matsayin shugaban jam’iyya, George yace tun da Arewa aka kai tuta, babu adalci idan Ayu ya ki murabus.

Vanguard tace a wani tsohon bidiyo da aka bankado, an ji Iyorchia Ayu yana mai alwashin zai sauka daga mukamin da yake kai idan aka ba Arewa tuta.

Kara karanta wannan

Bayan Wata 4 rak a Ofis, An Soma Yunkurin Raba Adamu da Shugabancin APC

Magana ta canza a yau

Da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Arise, shugaban jam’iyyar hamayyar ya yi wannan alkawari bayan an yi zaben shugabannin PDP na kasa a 2021.

Bisa dukkan alamu Dr. Ayu ya canza ra’ayinsa bayan ya gyara zama a kujerar jam’iyya, ya hakikance cewa babu abin da zai sa ya rubuta murabus.

Simon Imobo-Tswam wanda ke magana da yawun bakin shugaban jam’iyyar ya kafa hujja da dokar PDP, yace don haka babu dalilin canza shugaba a yanzu.

Fushin 'Yan takaran APC

An samu rahoto cewa wasu ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC sun nemi a dawo masu da kudin da suka kashe wajen sayen fam domin shiga takarar kujerun NWC.

Bayan wadannan ‘Yan siyasa sun kashe miliyoyin kudi, jam’iyyar APC ba ta bari an yi zabe ba, sai aka tsaida shugabanni na kasa ta hanyar maslaha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng