Da Yuwuwar Shekarau Ya Sauya Sheka Daga NNPP a Makon Nan, Kakaki
- Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce zai yanke shawarin sauya sheka daga NNPP ƙafin karshen makon nan
- Rahotanni sun bayyana cewa yan takarar shugaban ƙasa na manyan jam'iyyu na cigaba da zawarcin tsohon gwamnan na Kano
- A halin yanzun, ana sa ran Bola Tinubu na jam''iyyar APC zai gana da Shekarau a yau Laraba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya, Mallam Ibrahim Shekarau, zai yi nazari ya yanke hukunci kan batun sauya sheƙa daga NNPP.
Mai magana da yawun Shekarau, Sule Ya'u, shi ne ya bayyana haka ranar Talata yayin da yake amsa tambaoyin jaridar Punch game da rahoton da ke yawo a kafafen watsa labarai.
Rahoton ya nuna cewa Sanatan zai gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ranar Laraba.
Shekarau ya yi takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar ANPP da ta rushe a zaɓen 2011 kuma yana cikin jagororin jam'iyyar da suka tattauna da shugabannin sauran jam'iyyu har aka yi maja APC a 2013.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A matsayin ɗaya daga cikin waɗan da suka kafa APC, Sanatan ya jagoranci dubbannin magoya bayansa sun koma NNPP bayan samun saɓani da Gwamna Ganduje kan jagorancin jam'iyya.
Amma a yanzun rikici ya shiga tsakaninsa da shugabannin NNPP da ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabiu Kwankwaso, kan yadda aka kasafta kujerun shugabanci.
Malam Yau, ya ce Sanata Shekarau da sauran waɗan da ke tsaginsa zasu duba baki ɗaya zaɓukan da suka zo kan teburin su gabanin babban zaɓen 2023.
Vanguard ta rahoto yana cewa:
"Kuna ganin tawaga-tawaga da ɗai-daikun mutane na tuntubarsa, ya gana da Peter Obi wanda ya ziyarce shi, Kashin Shettima ya ziyarce shi, Atiku sau biyu yana gana wa da shi, yanzu ga Bola Tinubu."
"Saboda haka muna tattara dukkan tayin da suka zo mana, bayan haka zamu zauna mu yi nazari sannan mu yanke hukunci."
Meyasa Bola Tinubu zai kai masa ziyara?
Da aka tambaye shi kan makasudin da yasa Bola Tinubu zai sa labule da Shekarau, Ya'u ya ce siyasa ce kawai.
"Babban jagora a ƙasa kamar Tinubu, ya ce yana son ganinka shin zaka ce masa a'a? Amma maganar gaskiya zancen ba zai wuce na siyasa ba. Abokin takarar Tinubu, Kashim Shetima ya zo har gidan Shekarau."
Haka nan da aka tambaye shi zuwa yaushe Shekarau zai yanke hukunci kan ko zai fice daga NNPP, ya ce, "Kafin karshen wannan makon."
A wani labarin kuma tsohon abokin shugaban Buhari ya yi hasashen wanda zai lasje zaɓen 2023, ya bayyana jihohin da zai yi nasara
Buba Galadima, babban jigon jam'iyya mai kayan marmari ya yi hasashen Kwankwaso zai lashe zaɓen shugaban kasa a 2023.
Tsohon makusancin shugaba Buhari ya bayyana yadda tsohon gwamnan Kano zai yi nasara a jihohin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng