Kungiyar Fulani Ga Miyetti Allah: Yanzu Mun Waye, Za Mu Zabi Cancanta a 2023

Kungiyar Fulani Ga Miyetti Allah: Yanzu Mun Waye, Za Mu Zabi Cancanta a 2023

  • Wata kungiyar kwararrun Fulani ta yi Allah-wadai da kalaman da wasu makiyaya suka yi na bata sunan Peter Obi a kwanakin baya
  • A cewar kungiyar kwararrun, kungiyar Miyetti Allah ba ta magana da muryar kabilar Fulani a Najeriya
  • Kungiyar ta kuma bayyana cewa Fulani a Najeriya za su kada kuri'a ne na cancanta da kuma gogewa a zaben 2023 mai zuwa

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, wata kungiyar kwararrun Fulani, Coalition of Fulbe Professionals in Africa (COFPIA), a ranar Litinin, 15 ga watan Agusta ta nisanta kanta daga wata sanarwa da Miyetti Allah Kautal Hure ta yi.

A baya dai kungiyar Miyetti Allah ta ce al’ummar Fulani ba za su goyi bayan takarar Peter Obi ba, inda ta bayyana shi a matsayin mutum mai tsananin kabilanci.

Yadda Fulani suka juyawa kungiyar Miyetti Allah baya
Kungiyar Fulani Ga Miyetti Allah: Yanzu Mun Waye, Za Mu Zabi Cancanta a 2023 | Hoto: oyonews.com.ng
Asali: UGC

Jaridar Punch ta rahoto cewa kungiyar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da duk wani furucin da kungiyar Miyetti Allah, tare da cewa Miyetti Allah ba ta magana da muryar kabilar Fulani.

Kara karanta wannan

Miyetti Allah Ta Ce Bazata Goyi Bayan Takarar Peter Obi ba Saboda Yana Da Kabilanci

COFPIA a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa Farfesa Mohammed Gidado da sakatariyarsa Hajiya Mairo Modibo ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Kungiyar Fulani a duk fadin Najeriya ba za ta makance da wannan maganar ta Miyetti Allah ta siyasa ba.
“Fulani a yanzu sun waye kuma ba za a yi amfani da su a matsayin kayan yada ra’ayin addini ba. Za mu wayar da kan jama'armu don kada kuri'ar cancanta da kwarewa a 2023.
“Ba za mu taba zabar duk wani dan takara da ba shi da wani abin da zai iya ba, mun yi wuce batun ra’ayin addini da kabilanci.
“Za mu zabi shugaban da zai magance talauci da matsananciyar yunwar da ta dami mutanenmu na tsawon lokaci. Za mu zabi shugaban da zai yaki rashin tsaro da duk wani himma da kauda son zuciya, ko wanene shi."

Kara karanta wannan

Buhari: Da zarar an yi kidaya a 2023, za a samu mafita ga matsalar rashin tsaro

Ina Fatan Ku Samu 200: El-Rufai Ga Masoya Peter Obi Masu Shirin Gangamin Mutum Miliyan 2 a Kaduna

A wani labarin, gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai, ya caccaki magoya bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour kan wani yunkuri na yin tattaki tare da mutum miliyan biyu a jihar.

Yayin da zaben 2023 ya rage watanni shida, magoya bayan Obi sun yi tattakin nuna goyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar Anambra.

A Kaduna kuwa, sun bayyana shirinsu na yin wannan tattakin neman goyon baya. Abdullahi Umar Zarma, wani dan a mutum Peter Obi ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa, za su yi tattakin mai daukar hankali na mutum miliyan biyu a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.