Abin da ya sa ba za ta yiwu a tunbuke Shugaban kasa ba inji Tsohon Sanatan PDP
- Ayodele Arise ya zanta da manema labarai a kan barazanar sauke Muhammadu Buhari a Majalisa
- Sanata Arise ya bayyana cewa Sanatocin jam’iyyar APC ba za su bari a tsige Shugaban kasar ba
- ‘Dan siyasar yace ya zama tilas Bola Tinubu ya dauki Musulmi saboda APC ta lashe zaben 2023
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Ayodele Arise wanda ya wakilci Arewacin jihar Ekiti a majalisar dattawa ya yi hira da Daily Trust a kan abubuwan da suka shafi siyasar kasar nan.
Sanata Ayodele Arise ya shaidawa manema labarai cewa jam’iyyar APC ta dauki Musulmi da Musulmi ne saboda karancin kiristoci a Arewacin Najeriya.
Bayan an yi tunani da kyau, Arise yace an fahimci dole a dauko Musulmin Arewa a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a APC idan za a ci zabe.
“Bayan lissafi da kyau, za ka gane cewa akwai Kiristoci masu tunani da basira, amma abin tambayar ita ce, kuri’a nawa za su iya kawowa a ci zabe?
“Don haka kafin a iya lashe zabe, musamman a Arewa, duk mai son mulki bai dace ya maida hankali kan addini, idan aka yi haka, za mu sha kasa.”
- Ayodele Arise
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari ba zai tsigu a Majalisa ba
A game da maganar tsige shugaba Muhammadu Buhari a majalisar tarayya, Sanata Arise yace barazanar banza kurum Sanatocin suke yi wa shugaban kasa.
Arise mai sa ran komawa majalisar dattawa a 2023 yace sauke shugaban kasar ba zai yiwu ba domin jam’iyyar APC ta ke rike da rinjaye yau a majalisa.
“Nayi imani cewa barazana cewa kurum. Ba za a iya yin komai ba domi APC ta ke da rinjaye a majalisar dattawa, kuma shugaban kasarsu ne.”
“Duk abin da shugaban Najeriya ya yi, mafitar ba sauke shi daga kujera ba ne. Idan aka duba, ana bukatar kuri’un biyu bisa ukun ‘yan majalisa.”
- Ayodele Arise
Jagoran na APC ya shaidawa jaridar cewa akwai bukatar Sanatocin su hada-kai da majalisar dattawa, kuma tsige shugaban kasar zai iya kawo cikas a 2023.
Idan APC ta kafa gwamnati a shekara mai zuwa, tsohon Sanatan yace Bola Tinubu zai iya ba kiristoci manyan mukamai a gwamnati da fadar shugaban kasa.
An tuna da Kyaftin Hosa Okunbo
Dazu kun ji labari cewa an yi taro domin tunawa da Marigayi Kyaftin Hosa Okunbo, Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya gabatar da takarda wajen bikin a Abuja.
Goodluck Ebele Jonathan ya yi magana a game da abin da ya jawo rashin hadin kai a shekarun 1960, sannan ya tabo batun siyasar 2023 da wanda za a zaba.
Asali: Legit.ng