Rikicin PDP A Kano Na Kara Dagulewa, Mohammed Abacha Ya Maka Jam'iyya Da INEC A Kotu Kan Takarar Gwamna

Rikicin PDP A Kano Na Kara Dagulewa, Mohammed Abacha Ya Maka Jam'iyya Da INEC A Kotu Kan Takarar Gwamna

  • Jam'iyyar PDP na fuskantar sabon rikici a sakamakon karar da dan tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya ya shigar a kotu
  • A cikin karar, Mohammed Abacha ya bukaci kotun ta hana PDP da INEC maye gurbinsa da wani dan takara a zaben fidda gwani na jam'iyyar
  • Mohammed ya kuma jam'iyyar na PDP ta bashi dama na musamman ta kuma tantance shi a matsayin mambanta

Jihar Kano - Mohammed Abacha, dan shugaban Najeriya na mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha ya shigar da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC da Jam'iyyar PDP kara a kotu.

Mohammed a cikin karar ya bukaci kotun ta hana INEC da PDP maye gurbinsa da wani dan takarar gabanin zaben gwamnan Jihar Kano da za a yi a 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Za Ka Iya Shan Kaye A Zaben 2023, Wike Ya Fada Wa Atiku

Mohammed Abacha.
Kano: Sabon Rikici Na Kunno Kai Yayin Da Mohammed Abacha Ya Maka PDP Da INEC A Kotu Kan Tikitin Takarar Gwamna. Hoto: Mohammed Abacha.
Asali: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa a wani takardar da ya gabatar a kotu, Mohammed ya kallubalance karar da Jafar Sani Bello, dan takara da ya zo na biyu a zaben fidda gwani na PDP, na cewa shi ba dan jam'iyyar PDP bane.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tunda farko, Mohammed ya shaidawa kotu cewa jam'iyyar PDP ta bashi dama ta musamman kuma an tantance shi a matsayin dan takara.

A karar da ya shigar a kotun ta hannun lauyoyinsa J.Y. Musa (SAN) da Reuben Atabo (SAN), Mohammed ya yi karar INEC, Sadiq Aminu Wali da Alhaji Shehu Wada Sagagi.

A cewar Mohammed, shine ya lashe zaben fidda gwani da jam'iyyar ta yi a ranar 25 ga watan Mayu wanda INEC ta hallarci zaben don sa ido.

Ya ce ya samu kuri'u 736 sannan mai biye masa Ja'afar Sani Bello ya samu 710 amma daga baya aka maye gurbin sunansa da na Wali.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wike Ya Yi Magana Kan Karar Da Aka Shigar Na Neman Tsige Atiku A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa

Mohammed ya kuma nemi kotun ta hana shugaban jam'iyyar na jiha, Sagagi ya dena gabatar da Wali a matsayin dan takarar gwamna na jam'iyyar a zaben 2023.

An dage fara sauraron shari'ar zuwa ranar 12 ga watan Satumban 2022.

Mohammed Abacha ya lashe zaben fidda gwanin PDP na gwamna a Kano

Tunda farko, mun kawo muku rahoton cewa Mohammed Abacha, dan marigayi tsohon shugaban kasa, Sani Abacha, ya lashe zaben fidda dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Kano.

Jami'ar zabe, Barista Amina Garba, ta ayyana Mista Abacha a matsayin wanda ya lashe zabe bayan ya samu kuri’u 736 wajen kayar da babban abokin hamayyarsa, Sani-Bello wanda ya samu kuri’u 710, PM News ta rahoto

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164