Bishop Kukah: Ban Yarda Da Tikitin Musulmi Da Musulmi Ba
- Babban limamin cocin Katolika na shiyyar Sokoto, Bishop Matthew Hassan Kuka ya ce shi bai amince da tikitin musulmi da musulmi da APC ta yi ba
- Tun bayar da Bola Tinubu dan takarar shugaban kasa na APC ya sanar da Kashim Shettima, shima musulmi a matsayin mataimakinsa, sun rika shan suka musamman daga kungiyar CAN
- Kukah lura cewa addini na da muhimmanci ga yan Najeriya kuma tikitin musulmi da musulmi ya saba wa al'adar shugabanci a kasar kuma koma baya ne ga hadin kan kasa
Matthew Kukah, Bishop din cocin Katolika na Sokoto, ya ce tikitin musulmi da musulmi da jam'iyyar APC ta yi koma baya ne ga cigaban da ake samu na hada kan yan kasa, The Cable ta rahoto.
Kukah ya yi wannan jawabin ne a hirar da aka yi da shi a Channels Television a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC ya zabi Kashim Shettima, wanda shima musulmi ne a matsayin mataimakinsa.
Hakan ya janyo suka daga masu ruwa da tsaki musamman kungiyar kiristocin Najeriya, CAN.
Da ya ke magana kan batun, Kukah ya ce ana bawa tikitin shugaban kasa na musulmi da musulmi na 1993 'kimar da ya wuce misali' wurin nuna cewa yan Najeriya ba su damu da addini ba.
"A matsayi na na kirista, ina alfahari da rawar da muka taka wurin ganin an tafi tare da kowa a bangaren siyasarr Najeriya," in ji shi.
"A 1983, lokacin da Janar Buhari ya zama shugaban kasa, ya zabi Idiagbon. Duk da haka, yan Najeriya sunyi murna. Watakila nan ya kamata mu koma mu yi nazarinsa a matsayin inda laifin ya faru.
"Hakan ya saba wa al'ada baki daya. Batun shine musulmi biyu daga arewa za su mulki Najeriya, amma yan Najeriya suka basu wannan damar.
"Ina ganin muna fassara abin da ya faru a 1993 ta hanyar da bata dace ba saboda muna yaudarar kanmu cewa hakan hujja ne da ke nuna yan Najeriya ba su damu da addini ba.
"Tambayar da na ke yi wa abokai na musulmi, musamman yan arewa shine: 'Shin musulmin arewacin Najeriya sun shirya yin irin abin da kirista suka yi a 1984 da 1993?'"
Bishop din na Sokoto ya ce idan da abubuwa na tafiya yadda suka kamata ba dole ne a bada muhimmanci kan addinin shugabannin da za a zaba ba amma idan aka yi la'akari da irin nade-naden da aka yi a shekaru 7 da suka shude a gwamnatin nan, dole ya zama abin damuwa.
"A matsayi na na kirista, wannan abin zargi ne. Ban amince da shi ba, amma hakan APC ta zabi yi. Watakila, idan an fara kamfen, za mu ji abin mutane za su ce.
"Amma hakan ya zama ginshiki kuma zai mayar da mu baya bayan nasarorin da muke tunanin mun samu wurin hadin kan kasa," in ji shi.
2023: Ba Za Mu Bari Mambobin Mu Su Zabi Musulmi Da Musulmi Ba, In Ji Matasan Kungiyar CAN
Tunda farko, Kungiyar Kirista ta Najeriya, CAN, reshen matasa ta ce babu yadda za ta yi ta bari mambobinta su zabi musulmi da musulmi a matsayin shugaban kasa a zaben 2023, rahoton Vanguard.
Shugaban kungiyar, yankin arewa ta tsakiya, Owoyemi Alfred Olusola, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a Abuja a ranar Talata, ya ce matasan kirista sun yanke shawarar ba za su goyi bayan hakan ba.
Asali: Legit.ng