Jam'iyyar APC Ta Tagayyara Rayuwar 'Yan Najeriya, In Ji Tsohon Minista
- Bolaji Abdullahi, tsohon ministan wasanni da cigaban matasa na Najeriya ya shawarci yan Najeriya su juya wa jam'iyyar APC baya a 2023
- Abdullahi ya ce jam'iyyar ta APC mai mulki ta tagayyara rayuwar Najeriya don haka idan ana son sauya akalar kasar dole a tabbatar an fatattake su daga mulki
- Dan takarar na kujerar sanata na Jihar Kwara a karkashin jam'iyyar PDP ya yi wannan jawabin ne yayin taron kungiyar yan jarida da aka yi a Ilorin
Kwara - Tsohon Ministan Wasanni da Cigaba Matasa, Bolaji Abdullahi, a ranar Laraba ya bukaci yan Najeriya su fatattaki jam'iyyar APC a zaben 2023, yana mai cewa jam'iyyar ta tagayyara rayuwar yan kasar.
Tsohon ministan ya ce zaben 2023 ya bawa yan Najeriya wani dama na tabbatar da cewa sun zabi wadanda za su saita kasar, Punch ta rahoto.
Ya ce za a iya cimma burin bunkasa Najeriya ne kadai idan yan kasa, ta hanyar zabe, sun fatattaki yan siyasa da ke jam'iyyar APC.
Abdullahi, dan takarar Sanata na PDP, a zaben 2023 ya yi wannan jawabin ne a wurin taron 'yan jarida' karo na 33 na Kungiyar Yan Jarida Na Jihar Kwara a Ilorin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya yi magana kan babban aikin saita Najeriya
Abdullahi ya ce:
"Gwamnatin APC ta durkusar da Najeriya a gwiwowinta. Duk abin da muke tunanin ba za su faru ba sun faru a shekaru bakwai da suka shude. Babu yadda za a wanke APC daga matsalolin kasar nan.
"APC ta lalata kasar nan. Ya kamata yan Najeriya su juya wa dukkan yan takarar APC baya. Shekarar 2023 wata sabuwar dama ne na saita Najeriya."
Ya cigaba da cewa dukkan yan Najeriya na rayuwa cikin tsoro saboda rashin tsaro ga kuma talauci, yana mai kira ga yan kasar su dena maganin kansa ta hanyar rufe shi da bandeji.
Fitaccen Gwamnan APC Ya Kori Hadimansa Da Wasu Masu Rike Da Mukaman Siyasa
A wani rahoto daban, kun ji cewa Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti ya sallami wasu daga cikin hadimansa da wasu masu rike da mukaman siyasa.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa wadanda aka sallama cikin hadiman gwamnan sun hada da mashawarta na musamman, direkta janar, da shugabannin wasu hukumomin da ba karkashin minista suke ba da sauransu.
An sanar da hakan ne cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Mr Adejumo, sakataren dindindin na ofishin sakataren gwamnatin jihar.
Asali: Legit.ng