Aikin 'Yan Najeriya ne Tsige Buhari, Ba 'Yan Majalisa ba, inji Dan Siyasar Amurka
- Wani fitaccen dan siyasar jam’iyyar Republican a Amurka, Saul Anuzis, ya caccaki matakin da ‘yan adawa suka dauka na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Yayin da yake zargin Majalisar Dattijai a kasarsa da rashin adalci, Anuzis ya yi tsokaci cewa masu kada kuri'u ne kadai ke da hakkin tsige shugaba
- Anuzis ya kuma bayyana karara cewa, shugaba Buhari ya samu ci gaba sosai a yaki da ta'addanci a Najeriya, inda ya bukaci 'yan majalisa da su marawa gwamnatinsa baya
FCT, Abuja – Wani dan siyasar jam’iyyar Republican daga Amurka, Saul Anuzis, a ranar Laraba, 10 ga watan Agusta, ya ce tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari ba aikin ‘yan siyasar jam'iyyun adawa bane illa na masu kada kuri'u a kasar.
Dan siyasar na jam’iyyar Republican ya yi ikirarin cewa ‘yan siyasa masu kokarin tsige Buhari na kokarin jefa dimokuradiyya ne kanta cikin hadari, inji rahoton Punch.
‘Babban dan jam’iyyar Republican a Amurka ya yi ba’a ga yunkurin tsige Shugaba Buhari, inji Fadar Shugaban Kasa
Dan siyasar ya bayyana hakan ne a cikin wata maqala da aka buga a Washington Times ranar Talata, mai taken "America’s Newest Export: Impeachment Proceedings"
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ranar Laraba, 10 ga watan Agusta, fadar shugaban kasa ta fitar da wannan tsokaci a cikin wata sanarwa mai taken: 'Babban Jami’in Jam’iyyar Republican na Amurka ya yi ba'a da yunkurin tsige Shugaba Buhari', PM News ta kawo.
Anuzis ya ce majalisar dattawan Amurka ta kafa wani misali mara kyau ta hanyar tsige tsohon shugaban kasarta Donald Trump har sau biyu tare da hukunta shi ta hanyar shari’ar da aka yi ranar 6 ga watan Janairu.
Me yasa FBI ke binciken Trump?
Batutuwa da suka gabata a kotu sun kai ga FBI ta farmaki gidan Trump na Florida a ranar Litinin, 8 ga Agusta.
Wannan ra'ayi ya fadada muhawarar siyasa game da karuwar binciken shari'a na Trump a Amurka yayin da yake shirin sake tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben 2024.
Ya jaddada cewa shugabannin adawa ne ke da alhakin tuhumar masu rike da madafun iko tare da taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu bisa ga tsarin mulki.
Sanata Daga Arewa Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Baya Goyon Bayan Tsige Buhari
A wani labarin, shugaban kwamitin labarai da wayar da kan kasa na majalisar dattawa, Danladi Sankara ya nesanta kansa daga shirin da ake yi na tsige Shugaba Muhammadu Buhari, rahoton Daily Trust.
Sanata Sankara, wanda ke wakiltar Jigawa North West a Majalisar ya kuma nesanta kansa daga shirin tsige shugaban majalisa, Ahmad Lawan.
Tinubu na kawai karfe 4 na dare bai yi barci ba yana aiki saboda tsananin kwazonsa , Shugaban matasan APC Dayo Isarel
Sanatocin jam'iyyun adawa, a ranar Laraba, bayan tattaunawa na away biyu sun bawa Buhari wa'adin wata shida ya magance matsalar tsaro ko kuma su tsige shi.
Asali: Legit.ng