2023: Abubuwa 5 da za su taimakawa Peter Obi a kan Tinubu, Atiku da Kwankwaso

2023: Abubuwa 5 da za su taimakawa Peter Obi a kan Tinubu, Atiku da Kwankwaso

  • Masu fashin baki da nazarin siyasa suna ganin Peter Obi zai iya bada mamaki a zabe mai zuwa
  • Akwai dalilan da ke nuna ‘Dan takaran shugaban kasar zai iya mamayar manyan ‘yan siyasa
  • Zai yi wahala a iya hasashen abin da zai faru a 2023 saboda zaben wannan karo ya sha bam-bam

Rahoton Legit.ng ya kawo bayani game da abubuwan da za su taimakawa Peter Obi da jam’iyyar LP a zaben shugaban kasa da za ayi a 2023.

1. Salon kamfe

Peter Obi yana kokarin gujewa taba abokan gabarsa, a duk lokacin da aka zanta da shi, yana maida hankali ne a kan abubuwan da suka shafi cigaban al’umma.

Mafi yawan lokuta, ‘dan takaran ya kan tabo batun rashin ilmi, talauci, lantarki, rashin tsaro da sauransu. Amma wasu na ganin bai fahimci matsalolin da kyau ba.

Kara karanta wannan

Duk bula ce: Ainihin Abin da ya sa Ake Barazanar Sauke Buhari inji Dan Majalisa

2. Tarihi

Magoya bayan Peter Obi suna tinkaho da cewa gwanin na su yayi abin da za a yaba a lokacin da ya yi gwamnan jihar Anambra, musamman ta fuskar kula da tattali.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Masu kaunar ‘dan siyasar suna ganin idan ya samu mulkin kasa, ba za ayi facaka da dukiyar al'umma ba. Masu adawa na watsi da kokarin gwamnatin Obi a Anambra.

Peter Obi, Tinubu, Atiku da Kwankwaso
Obi, Tinubu, Atiku da Kwankwaso Hoto: @PeterGregoryObi, @KwankwasoRM
Asali: Facebook

3. Matasa

Legit.ng ta fahimci Obi ya shahara wajen matasa wadanda suke ganin ‘dan takaran ya bambanta da abokan gabarsa. ‘Yan tafiyar EndSARS sun yi na’am da shi.

4. Rikicin cikin gida

Jam’iyyar APC ta samu rabuwar kai saboda tsaida Musulmi-Musulmi, ita kuwa PDP ta samu baraka a dalilin rikicin Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike.

Sabanin da ya shiga tsakanin manyan jam’iyyun APC da PDP zai iya taimakawa LP a wasu jihohi. Legit.ng Hausa na tunanin wannan zai fi tasiri a kudancin kasar nan.

Kara karanta wannan

Tinubu na kawai karfe 4 na dare bai yi barci ba yana aiki saboda tsananin kwazonsa , Shugaban matasan APC Dayo Isarel

5. Addini

Akwai yiwuwar addini ya yi tasiri a zaben 2023, a manyan ‘yan takaran shugaban kasa, Peter Obi ne kurum kirista. Sauran jam’iyyun duk sun tsaida musulmi ne.

Ganin Muhammadu Buhari wanda musulmi ne yayi shekaru takwas a mulki, LP za ta iya samun karbuwa ga masu zargin cewa an yi watsi da su tun daga 2015.

Alaka da kungiyar asiri

Kun ji labari cewa ana zargin ‘dan takaran LP, Peter Obi yana da alaka da kungiyar Pyrates Confraternity, wanda ake yi wa kallon kungiyar 'yan asiri.

Hadiminsa, Valentine Obienyem ya karyata wannan zargi, yace Obi bai da wani hadi da tafiyar Pyrates Confraternity kamar yadda wasu ke ta yadawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng