Jerin jiga-jigan PDP da zasu zama yan kallo a zaben 2023

Jerin jiga-jigan PDP da zasu zama yan kallo a zaben 2023

  • Wasu wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP za su zama yan kallo a lokacin gudanar da zabe saboda basa cikin yan takara a zaben 2023 dake zuwa
  • Jiga-jigan jam’iyyar PDP baza su samu damar tsayawa takara ba saboda sun sha kaye a takarar neman mukamai daban-daban a lokacin zaben fidda gwani
  • Gwamnan Jihar Rivers Nyesome Wike, Shine Dan Siyasan Na Farko da zai zama dan kallo a zaben 2023

A zabe mai zuwa na 2023, sunayen wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP ba za su kasance a cikin tikitin takara ba. Rahoton Legit.NG

Hakan ya faru ne saboda sun sha kaye a takarar neman mukamai daban-daban a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar. Gwamna Wike ne ke kan gaba a jerin fitattun jiga-jigan PDP da suka sha kaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Kara karanta wannan

APC Ta Faɗi Sunan Wani Gwamnan PDP Dake da Hannu a Matsalar Tsaron Jiharsa, Ta Nemi a Kayar da Shi a 2023

Ga jerin fitattun ‘ya’yan PDP shida a wannan fanni.

1. Gwamna Nyesom Wike

Gwamna Nyesom Wike, Gwamnan Jihar Ribas, wanda zai kammala wa'adinsa na biyu a 2023, ya nemi tsayawa takarar Shugaban kasa a 2023.

Sai dai ya kasa samun tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP; ya sha kaye a hannun tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar. Yayin da Atiku ya samu kuri'u 371 daga cikin wakilai 767 na kasa da aka amince da gudanar da aikin, Wike ya samu kuri'u 237 ya zo na biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Sanata Shehu Sani

Bayan ya koma PDP daga PRP, Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar wakilai ta 8, ya yi burin mulkin jihar Kaduna a sabuwar jam'iyyarsa. Sai dai ya kasa samun tikitin takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar. Tsohon Sanatan ya sha kaye ne a hannun Isah Ashiru wanda tsohon dan majalisar wakilai ne.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa A Rikicin PDP, Gwamna Wike Da Atiku Abubakar Sun Cimma Wata Matsaya Ɗaya

Power
Jerin jiga-jigan PDP da zasu zama yan kallo a zaben 2023 FOTO Legit.NG
Asali: Facebook

3. Sanata Dino Melaye, tsohon dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma a majalisar wakilai ta 8, shi ma ya rasa tikitin PDP na komawa majalisar dattawa a 2023. Ya sha kaye a hannun Tajudeen Yusuf, dan majalisa mai wakiltar mazabar Kabba/Bunu Ijumu na tarayya a halin yanzu. . Yusuf wanda ya samu kuri'u 163, ya doke Dino wanda ya samu kuri'u 99.

4. Istifanus Gyang Sanata mai wakiltar Filato ta Arewa, Istifanus Gyang shi ma ya sha kaye a zaben fidda gwani na jam'iyyar a hannun dan majalisar tarayya mai wakiltar Barkin Ladi/Riyom Federal Constituency Hon. Simon Mwatkon. Sanata Gyang ya samu kuri'u 99 inda ya sha kaye a hannun Mwatkon wanda ya samu kuri'u 119.

5. Danjuma Laah mataimakin mai wakiltan marasa rinjaye, Danjuma Laah, shi ma ya rasa tikitin takarar sanatan Kaduna ta kudu a PDP. Sunday Katung, tsohon dan majalisar wakilai ne ya doke shi, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Ko ba Wike Zan iya nasara a zaben 2023, Atiku ya shaidawa Dattawan PDP

6. Adamu Sambo , dan tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, ya sha kaye a yunkurinsa na lashe tikitin takarar kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar Kaduna ta Arewa a hannun ‘yar majalisar wakilai mai ci, Samila Suleiman. A wani al’amari mai ban mamaki, Sambo ya bukaci wakilan da su mayar wa kowanne dan majalisa naira miliyan biyu da ya baiwa kowane wakilai kafin zaben fidda gwani bayan ya samu kuri’u biyu kacal.

Kamfanin Whatsapp Ta Yiwa Manhajjanta Karin Ka’aidojin Boye Sirri Guda 3

A wani labari kuma, WhatsApp zata gabatar da sabbin ka’idojin boye sirri guda uku a cikin manhajatta don kare sakonnin mutane, kamfanin ta sanar da haka a ranar Talata. Rahoton Legit.NG

A cikin wata sako da fitar shafin ta na yanar gizon, whatsapp wanda mallakar kamfanin Meta ce ta bayyana cewa sabon fasalin zai baiwa masu amfani da shi iko akan tattaunawar su akan manhajjar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel