Duk bula ce: Ainihin Abin da ya sa Ake Barazanar Sauke Buhari inji Dan Majalisa
- Hon. Adejoro Adeogun ya bayyana cewa da kamar wuya ayi nasarar tunbuke Shugaban Najeriya
- ‘Dan Majalisar yace Sanatocin PDP sun kawo yunkurin ne domin su samu hanyar lashe zaben 2023
- Wasu ‘Yan Majalisa sun ba Muhammadu Buhari wa’adin makonni shida ya kawo karshen rashin tsaro
Abuja - A wata hira ta musamman da aka yi da Adejoro Adeogun a Punch, ya yi bayanin abunuwan da suka shafi sha’anin tsaro da siyasar 2023.
Honarabul Adejoro Adeogun shi ne mataimakin shugaban kwamitin tsaro a majalisar wakilan tarayya, kwararren ‘dan siyasa, kuma jigo a APC.
Da aka jefawa ‘dan majalisar tambaya a game da yunkurin da ake yi na sauke shugaba Muhammadu Buhari, sai yace dabarar cin zabe ne kurum.
An rahoto Adeogun yana cewa Sanatocin PDP sun zo da wannan ne domin su samu nasara a 2023.
"Son a sani ne ba komai ba."
Marasa rinjaye suna yin aikinsu – su yi wa gwamnati adawa da kyau. Ka tuna cewa saura ‘yan watanni a fara babban zabe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Saboda haka ‘yan adawa na bukatar su samu damar shiga kafafen yada labarai da nufin su tallata ‘yan takaransu da kyau.”
- Hon. Adejoro Adeogun
Lokaci ya kure yanzu
‘Dan majalisar na yankin Akoko yace Sanatoci sun san da kamar wuya a iya kawo kudirin sauke shugaban kasa, kuma ayi nasara domin lokaci ya kure.
Haka zalika Adeogun yace sauke Mai girma shugaba Muhammadu Buhari daga mulki za iyi wahala saboda irin rabuwar kan da ake da shi a Najeriya.
“Saboda haka siyasa ce kurum. Duk wani ‘dan majalisar tarayya ya san tanadin da doka tayi wajen tunbuke shugaban kasa.
An san da wahala a iya sauke shugaban kasa watanni ga zabe, musamman a kasa mai rabuwar kai irin Najeriya.”
- Hon. Adejoro Adeogun
Baraka a shirin 2023
Kwanaki aka samu rahoto cewa North Central APC Forum ta bukaci Gwamnan Filato cewa ka da ya sake ya jagoranci kwamitin neman zaben Bola Tinubu.
Kafin a je ko ina, shugaban kungiyar nan, Saleh Mandung Zazzaga ya nuna ‘Yan Arewa maso tsakiya sun raina kujerar Darektan kamfe a jam’iyyar APC.
Asali: Legit.ng