Gwamna Wike Ya Nunawa Atiku Alamar Mutanen Ribas ba Za Su Zabi PDP ba
- Nyesom Wike ya gayyaci Gwamnan Legas domin kaddamar da wasu ayyuka da ya yi a jihar Ribas
- Gwamnan jihar Ribas ya bayyana cewa a 2023, mutanensa ba za su zabi duk wanda ya raina su ba
- Wike ya ja-kunnen masu neman kuri’un Ribas a zabe mai zuwa, ya tuna masu shi ne a kan mulki
Abuja - A ranar Litinin, 8 ga watan Agusta 2022, alamu suka fara nuna yiwuwar sasanta Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike ya gamu da matsala.
A rahoton da muka samu daga jaridar Punch, an ji Mai girma Nyesom Wike ya na nuna a 2023, mutanen jihar Ribas ba za su zabi wanda ya yi watsi da su ba.
Yayin da yake kaddamar da gadar Orochiri-Worukwo, Gwamnan na Ribas ya bayyana cewa mutanensa ba za suyi asarar kuri’un a zaben shugaban kasa ba.
Jaridar tace Gwamnan yana shagube ne ga Atiku Abubakar da shugabannin jam’iyyar PDP na kasa, yake cewa su daina tunanin samun kuri’un jihar Ribas.
Abin da Nyesom Wike ya fada
“Idan ku kace jihar Ribas ba ta da tasiri, idan lokacin da ya kamata ya zo, Ribas za ta nuna maku cewa lallai ku ma ba ku da tasiri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba ku kaunarmu, mu ma ba mu kaunarku. Idan ka na kaunarmu, mu na kaunarka. Ba za mu yi asarar kuri’a haka kurum ba.”
“Kuri’unmu za su yi tasiri a zabe. Kuma za mu amfana da kuri’un duk wanda za mu marawa baya.
Ni ke rike da mulkin Ribas
The Cable ta rahoto Gwamnan yana cewa yanzu siyasa ta canza, ba za su zabi ‘dan takara haka kurum ba, sai idan har sun tabbata za su amfana da mulkinsa.
Nyesom Wike yake cewa zai yi wahala wani ya iya canza yadda mutanen jiharsa ke yin zabe. Gwamnan ya kuma ja-kunnen masu neman gwamna a jihar.
“Babu wanda zai ci zabe a nan, wadanda suka saci dukiyar kasa ba su isa su zo nan Ribas su zama gwamnoni ba, kuma na kalubalance su.”
“Ni ke da mulki a nan. Ni ba irin gwamnonin da za a je Abuja, a shirya taro domin a yake nib a ne. Ni na ke rike da madafan iko a nan.”
Abin mamakin shi ne Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ne ya kaddamar da ayyukan da Wike ya yi. Kafin yanzu ba a ga maciji tsakanin Wike da APC.
Asali: Legit.ng