‘Danuwan Buhari ya Fadawa Duniya Wanda ya yi Dalilin Barinsa Jam’iyyar APC

‘Danuwan Buhari ya Fadawa Duniya Wanda ya yi Dalilin Barinsa Jam’iyyar APC

  • ‘Dan majalisa mai wakiltar mazabun Daura/Sandamu/Mai Adua ya fadi abin da kai shi sauya-sheka
  • Fatuhu Muhammed yake cewa zamansa a APC ya zo karshe tun da abokin gaba ya ci masa mutunci
  • ‘Dan siyasar ya zargi abokin fadansa, Dr. Aminu Jamoh da zagin mahaifinsa da sunan ana yin siyasa

Katsina - Fatuhu Muhammed, mai wakiltar Daura/Sandamu/Mai Adua a majalisar wakilan tarayya ya fadi abin da ya jawo ya sauya-sheka daga APC.

A ranar Litinin, 8 ga watan Agusta 2022, Daily Trust ta rahoto Honarabul Fatuhu Muhammed ya na bayanin yadda abokin adawa ya ci masa mutunci.

Da aka zanta da shi a ranar Lahadi, ‘dan siyasar yace abokin takararsa a zaben fitar da gwani, ya zagi mahaifinsa ne, a dalilin haka shi ya canza sheka.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gida: Bayan Shan Kaye, Ɗan Uwan Shugaba Buhari Ya Fice Daga Jam'iyyar APC

Idan an zagi Bafallo, an zagi Buhari

“Na saurari wani faifen murya inda ‘dan takararsu (Jamo), ya kama sunan mahaifina, Alhaji Mamman Dan Bafallo, ya tirka masa zagi.
Alhaji Mamman Dan Baffallo da Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, dukkaninsu uwarsu daya kuma ubansu daya."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Danuwan Buhari
Fatuhu Mohammed da magoya bayansa Hoto: @ahmad.ganga.545
Asali: Facebook

Baffallo da Buhari 'yanuwan jini ne

"A cikin ‘ya ‘ya 26 da ubansu ya haifa a Duniya, su biyu (Mamman Dan Bafallo da Buhari) ne kurum suke uwa daya da uba daya.
Saboda haka zagin mahaifina tamkar zagin shugaban kasar ne.”

An fara fita daga adawar siyasa

Ganin yadda adawar siyasa ta kai ana taba asalinsa, sai Hon. Fatuhu Muhammed ya ce babu dalilin da zai cigaba da zama a APC tare da su Aminu Jamo.

“Saboda haka sai na ce abin ya wuce siyasa idan ana cin mutuncin iyayena. Ba zan iya daukar wannan ba

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: Jami'an NDLEA Sun Kama Wani Soja Mai Ritaya Ɗan Shekara 90 Dake Kaiwa Yan Bindiga Kwayoyi

Kuma zama a APC ba tilsas ba ne. saboda sai na yanke hukuncin in fita daga jam’iyyar.” - Fatuhu Mohammed.

Ya taba 'Dan Baffalo - Mai bada shawara

Ahmed Ganga, hadimin 'dan majalisar ya nuna hoton tattaunar Fatuhu Mohammed da wanda APC ta ke sa ran zai maye gurbinsa a zabe mai zuwa.

Daga hirar ta Whataspp, za a fahimci 'Dan majalisar tarayyar ya shaidawa Dr. Jamo cewa ta bangarensa, babu abin da zai sa shi ya zagi mahaifinsa.

PDP da su NNPP na zawarci

Kwanakin baya Muhammad ya tabbatar da cewa magana tayi nisa tsakaninsa da jam’iyyun hamayya yayin da ake tunanin zai tu waje daga APC.

‘Dan Majalisar na Daura, Sandamu da Mai Adua ya na duba yiwuwar ficewa daga APC mai mulki tun da ya gagara samun tikitin tazarce a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel