Mummunar Rigima ta Kaure Kan Rabon Kudi Wajen Taron PDP, Ta Kai An Rasa Rai
- Sabani ya shiga tsakanin wasu bangarorin PDP a yankin Ede a jihar Osun, ta kai wani ya mutu
- Ana ta faman rikici ne sai wani ‘dan jam’iyya ya gayyato ‘yan sanda, ana hakan aka harbe wani
- Rahotanni sun ce ‘ya ‘yan jam’iyyar suna rigima ne a kan batun kudin da aka raba zaben gwamna
Osun - Ana zargin wani Bawan Allah wanda aka bada sunan shi a matsayin Kuranga, ya mutu a wajen wata rigima da ta barke a taron jam’iyyar PDP.
Wani rahoto da ya fito daga Punch ya nuna cewa rikici ya kaure tsakanin wasu magoya bayan PDP a mazabar Oloba da ke yankin Atapara, jihar Osun.
Wata majiya tace rikicin da ya barke bai rasa alaka da rabon kudi. Daga nan sai aka ji harbe-harben bindiga da tayi sanadiyyar mutuwar Kuranga wajen taron.
Rahoton yace bayan lamarin ya rincabe, daya daga cikin wadanda ake rigima da su ya dauko jami’an ‘yan sanda domin su kama wasu ‘ya 'yan jam’iyyar.
“A kokarin kama mutane ne aka harbi Kuranga. Amma ba zan iya cewa ga wanda ya harbe shi ba. Abin ya faru ne a ranar Juma’a.”
- Wata majiya a Ede
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka aka yi - NSCDC
Da aka zanta da mai magana da yawun bakin jami’an NSCDC ta reshen jihar Osun, Olabisi Atanda, ta tabbatar da cewa an rasa rai a taron da ya gudana.
“An yi taron jam’iyyar PDP, sai aka samu rashin fahimta a game da batun kudin da aka raba na zaben gwamnan Osun da ya wuce.”
“An samu takaddama tsakanin jama’a a taron, sai wani daga cikin mahalartar ya kira ‘yan sanda zuwa wajen taron domin cafke su.”
“Ana haka ne sai aka harbi wani da ake kira Kuranga. Ba zan iya tabbatar da ya mutu ko bai mutu ba. Lamarin dai ya jawo hatsaniya.”
Sharrin ‘Yan APC ne – Jigon PDP
Da aka nemi aji ta bakin ‘yan sanda ba, kakakin dakarun jihar Osun, Yemisi Opalala ba ta amsa kiran wayar ta ba, kuma an ji shiru bayan aika mata sako.
Wani jami’in PDP na reshen jihar, Oladele Oluwabamiji ya zargi shugabannin APC da kawo tsageru wajen taron jam’iyyar hamayyar, wanda suka tada fitina.
Oluwabamiji yace wani ‘dan majalisa na APC ya halarci taron. Kawo yanzu, jami’an tsaro sun shaida cewa abubuwa sun dawo daidai a karamar hukumar.
APC ta murde zaben 2019
A jiya aka ji Sanatan jihar Ogun, Ibikunle Amosun yace ba ‘Dan takaran APC ya lashe zaben da aka yi a 2019 ba, amma ya nuna abin da ya wuce ya wuce.
Amosun ya yi ikirarin wadanda suka murde zaben Gwamnan a Ogun sun nemi afuwarsa, amma yace dole a kifar da gwamnatin APC mai-ci a 2023.
Asali: Legit.ng