Zabe za a yi ba 'wuruwuru': Shirin da Buhari ke yi gabanin babban zaben 2023
- Gwamnatin Buhari ta ba ‘yan Najeriya tabbacin gudanar da sahihin zabe na gaskiya da adalci gabanin babban zaben 2023 da ake sa ran za a yi
- Shugaba Buhari ya ba ‘yan kasar wannan tabbacin ne ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya)
- A cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, babu wani nau'i na 'wuruwuru' da za a amince da shi a karkashin kulawar sa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa ba zai bari a yi magudin zabe ko rashin da’a a karkashin kulawarsa ba a zaben 2023 mai zuwa.
Shugaban ya fadi haka ne a wani taron karawa juna sani kan harkokin tsaro na ‘Election Security Management’ wanda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta shirya a Abuja.
Rashin Tsaro: Za Mu Raba Lawan Da Kujeransa Idan Ya Kawo Mana Cikas Wurin Tsige Buhari, In Ji Sanatan Najeriya
Shugaban ya samu wakilcin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), inda ya ba da tabbacin cewa babu wata jam’iyyar siyasa ko wani mutum da zai zo da wargi a lokacin zabe.
Monguno ya kuma ce shugaban kasar ya umarci dukkanin jami’an tsaro a fadin kasar nan da suka hada da hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) da su yi aiki tare ta hanyar duba duk wasu dabarun gudanar da zabe sahihi a badi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Vanguard ta rahoto cewa Monguno ya lura cewa taron horon kan harkokin tsaro na zabe da babban sufeton ‘yan sanda ya shirya na zuwa ne a lokacin da ake bukatarsa.
A kalamansa:
“Hakazalika, zai kara karfin daidaita kalubalen tsaro na cikin gida da ake fuskanta a halin yanzu, wajen samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasa domin su yi amfani da ikonsu.
"Zabe cikin nasara tare da tsarin 'yan sanda da lumana wani muhimmin canji ne a kokarin kowace kasa na ci gaban dimokuradiyyarta da zurfafa romon dimokuradiyya."
'Yan sanda ke jagorantar gudanar da zaben nagari
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa yayin da yake karin haske, Monguno ya ce kasancewar ‘yan sanda ne ke kan gaba wajen gudanar da ayyukan zabe, dole ne a kula da rahotannin sirri da sauran muhimman ayyukan da hukumomi ke yi da gaske.
Ya kara da cewa:
“Dole ne in nanata cewa Shugaban kasa yana jajircewa wajen ganin an gudanar da zabe mai cike da aminci kuma wanda zai ba umarnin karbuwar al’ummar Najeriya baki daya.
“Wannan zaben a wurin shugaban kasa, ba zai samu nakasu ba, a lafuzzan 'yan Najeriya, babu ‘Wuruwuru’.
Zai yi abin da yake so: FG ta ba dalilin da yasa Buhari zai ba jamhuriyar Nijar motocin N1.5bn
A wani labarin, gwamnatin tarayya, a ranar Laraba, ta kare kudurin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kashe Naira biliyan 1.145 ga Jamhuriyar Nijar, Daily Trust ta ruwaito.
Ministar Kudi, Kasafin da Tsare-Tsare ta Kasa Zainab Ahmed, ta yi wannan tsokaci ne a lokacin da ta ke gabatar da tambayoyi bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban kasa ya jagoranta a fadar gwamnati da ke Abuja.
Ministar, wacce ta ce shugaban kasar na da ‘yancin yanke shawara don amfanin Najeriya, ta kara da cewa "wannan ba shi ne karon farko da kasar ke ba da irin wannan gudunmawa ga makwabtanta ba."
Asali: Legit.ng