2023: Ana Kokarin Kawo Karshen Rikicin Jam’iyyar PDP, Atiku Ya Zauna da Wike
- Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya zauna da Atiku Abubakar da nufin ayi sulhu a jam’iyyar PDP
- ‘Dan takaran Shugaban kasar ya hadu da tsohon abokin hamayyarsa ne a gidan Farfesa Jerry Gana
- Manyan ‘yan siyasar sun sa labule ne a lokacin da aka ji majalisar BoT na kokarin dinke baraka
Abuja - A yammacin Alhamis, 4 ga watan Agusta 2022 ne aka yi wani zama domin ayi sulhu tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike.
Premium Times ta fitar da rahoto na musamman da ke cewa an yi wannan zama ne a gidan tsohon Ministan tarayya a Najeriya, Farfesa Jerry Gana.
Haduwar ‘dan takaran shugaban kasar da gwamnan na Ribas na zuwa ne jim kadan bayan ‘yan majalisar amintattu na BoT sun yi wani zama a Abuja.
BoT wanda ita ce majalisar koli na masu bada shawara a PDP sun sa baki a rikicin Atiku Abubakar da mutanen Wike wanda zai iya kawo cikas a 2023.
Abokan hamayya a daki daya
Legit.ng Hausa za ta iya cewa wannan ne karon farko da tsohon mataimakin shugaban Najeriyan ya kebe daga shi sai Wike a tsawon watanni.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Har zuwa yanzu da muke tattara wannan rahoto, ba mu san abin da ‘yan siyasar suka tattauna ba.
Baya ga haka, Atiku Abubakar da Nyesom Wike ba su fitar da wani jawabi a game da wannan haduwa ba. Kawo yanzu dukkaninsu ba suce uffan ba.
Akwai alamun nasara
Wasu jagororin jam’iyyar PDP da suka san yadda taron ya kasance, sun shaidawa jaridar cewa an fara samun nasara daga zaman da ‘yan siyasar suka yi.
Sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba ya nuna ana sa ran Atiku Abubakar da Nyesom Wike za su sasanta rigimar da ta shiga tsakaninsu.
Debo Ologunagba ya shaidawa manema labarai za a saurari yadda ta kaya a karshen rahoton da ‘yan majalsar BoT na PDP za su gabatarwa uwar jam’iyya.
Kafin yanzu an ji cewa Wike wanda ya sha kashi a zaben fitar da gwani na PDP yana ta sukar Atiku Abubakar da mutanensa, ya zarge su da yi masa sharri.
Masana siyasa na cewa PDP ta na bukatar kuri’un jihar Ribas kafin tayi nasara a 2023, idan aka yi la’akari da matsalar da za ta fuskanta a Legas da Kano.
An bada sharudan sulhu
A tsakiyar makon nan kuka samu labari ana sa ran majalisar amintattu na PDP watau BoT za tayi zama domin shawo kan sabanin da ake ta samu.
Tun bayan zaben fitar da gwani ake samun rikici tsakanin ‘dan takaran shugaban kasar da kuma Gwamnan jihar Ribas. wanda ya zo na biyu a zaben.
Asali: Legit.ng