An Fallasa Mutumin Da Ke Yi wa Bola Tinubu Zagon-kasa a Ministocin Buhari
- Ana tuhumar Ministan cikin gida da hannu a nasarar da PDP ta samu a zaben Gwamnan jihar Osun
- Matasan APC sun ce Rauf Aregbesola da mutanensa ba su goyon bayan Bola Tinubu a zaben 2023
- ‘Yan bangaren tsohon Gwamnan na jihar Osun a APC sun maidawa Goke Akinwemimo martani
Osun - Kungiyar matasa na jam’iyyar APC a jihar Osun, sun ayyana Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola da mutanensa a cikin masu yi wa jam’iyya barna.
A ranar Laraba, 3 ga watan Agusta 2022, Vanguard ta rahoto matasan su na zargin cewa Ministan da magoya bayansa sam ba su goyon bayan jam’iyyar APC.
Shugaban matasa na APC a jihar Osun, Goke Akinwemimo ya shaidawa manema labarai cewa akwai yiwuwar Aregbesola na kokarin ganin APC ta rasa zabe.
Da yake jawabi a jiya a sakatariyar APC a garin Osogbo, an rahoto Goke Akinwemimo yana cewa Ministan ne wanda ya kitsa zanga-zangar da aka yi wa jam’iyya.
'Yan taware suka ba PDP nasara
Ana ji ana gani, Aregbesola ya marawa ‘yan taware baya a zaben gwamnan Osun da aka gudanar kwanaki, Akinwemimo yace wannan ne ya jawowa APC cikas.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaban matasan ya nuna cikakkiyar goyon baya ga Gwamna Adegboyega Oyetola da kuma shugaban APC na reshen Osun, Hon. Prince Adegboyega Famodun.
Baya ga haka, Akinwemimo ya yi kira ga tsohon gwamnan ya guji ruguza jam’iyyar APC mai mulki.
Karya ake yi mana - Mutanen Aregbesola
Kakakin ‘yan taware na APC a Osun, Abiodun Agboola, ya yi watsi da wadannan zargi da aka jefi uban gidansun da shi, yace ba haka lamarin nan yake ba.
Agboola ya shaidawa manema labarai cewa suna goyon bayan Bola Tinubu a zaben shugaban kasa, yace wannan shi ne alkawarin da aka yi da ‘yan kungiyarsu.
Sannan sakataren yada labaran ‘yan APC na bangaren Aregbesola yace bai kamata a zarge su da hannu wajen nasarar da PDP ta samu a zaben Gwamnan jihar ba.
A cewar Agboola, APC tayi nasara a garin Aregbesola, amma ta fadi a garuruwan na-kusa da Gwamna.
Tsige Buhari daga mulki
Dazu aka ji Sanata Shehu Sani ya jero abubuwan da za su hana a iya sauke Shugaban Najeriya, yace za a bata lokaci ne kurum a banza ba tare da an yi nasara ba.
Kwamred Sani yace lokaci ya kure sosai, ya nemi Sanatocin PDP da ke Majalisa su karkata wajen ganin yadda za a kifar da Gwamnatin APC a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng