Kishin-kishin: Gwamnan Arewa Zai Jagoranci Yakin zaben Tinubu/Shettima

Kishin-kishin: Gwamnan Arewa Zai Jagoranci Yakin zaben Tinubu/Shettima

  • Babu mamaki a sanar da Simon Bako Lalong a matsayin shugaban yakin zaben Asiwaju Bola Tinubu
  • Gwamnan Filato za a nada a matsayin Darekta Janar na kwamitin da zai yi wa APC aikin kamfe a 2023
  • An cin ma matsaya ne bayan Bola Tinubu, Kashim Shettima da manyan APC sun yi zama a jihar Legas

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagos - Idan dai ba abubuwa sun canza daga baya ba, ana tunanin Simon Bako Lalong za a sanar a matsayin shugaban yakin zaben Bola Tinubu.

Rahoton da Daily Trust ta fitar a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta 2022 ya nuna cewa Gwamna Simon Bako Lalong ne zai zama Darekta Janar na kamfe.

An bada sunan Gwamnan na jihar Filato ya jagoranci yakin takarar Bola Tinubu da Kashim Shettima a zaben 2023 saboda irin babatun da wasu ke yi.

Kara karanta wannan

Elrufai Ya Ce APC ta Riga Ta Nada Darakata Janar Na Kamfen Din Takarar Tinubu Da Shettima

Ana korafi a kan yadda Bola Tinubu ya dauko wani musulmi, Kashim Shettima domin zama abokin takararsa. Abin da ba a taba gani ba tun 1993.

Kafin yanzu an samu labari cewa Malam Nasir El-Rufai shi ne wanda manyan APC suka zaba a matsayin Darekta Janar na yakin neman zaben na APC.

Har ila yau kuma an bada shawarar a dauki tsohon shugaban APC na kasa watau Adams Oshiomhole a matsayin shugaban majalisar yakin zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kaddamar da Shettima da Bola Tinubu
Kashim Shettima da Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Magana ta canza a APC

Amma daga baya sai Bola Tinubu ya yi zama da Kashim Shettima, shugaban kungiyar gwamnonin APC, da wasu gwamnoni da jagororin jam'iyya.

A wajen wannan taro na Legas aka cin ma matsaya Gwamnan Filato, Simon Lalong ya jagoranci kamfe domin a iya kwantar da hankalin kiristocin Arewa.

Kara karanta wannan

Wike ya Zauna da Gwamnonin PDP, ya Gindaya Sharadin Marawa Atiku Baya

Rahoton yace Tinubu da sauran kusoshin jam’iyyar APC mai mulki sun fara wannan taro ne tun a ranar Litinin cikin dare, ba a iya kammalawa ba sai a jiya.

Wata majiya daga wajen taron ta tabbatar da cewa Gwamna Lalong za a sanar a matsayin Darekta Janar, an kuma ji babu wani rabuwar kai a jam'iyyar.

Gwamnoni da manyan APC a taron

Abdullahi Ganduje (Kano), Atiku Bagudu (Kebbi), Abubakar Badaru (Jigawa), Bello Matawalle (Zamfara), da Babajide Sanwo-Olu (Legas) sun halarci taron.

Ragowar wadanda aka gani a wajen wannan zama sun hada da Iyiola Omisore, Adams Oshiomohole, Alhaji Kabiru Masari sai Gwamna Nasir El-Rufai.

Ba zan yi Tinubu ba

Jiya ku ka ji an samu mutum na biyu a APC da aka ji yana cewa zai zabi LP ne a maimakon ‘Dan Takaran Shugaban Kasar da Jam’iyyarsu ta tsaida.

Jigon APC, SKC Ogbonniya ya caccaki 'dan takaran 2023, yace babu wanda ya san gaskiya game da suna, asali, karatu, ilmi da silar azikin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Ana Tonon Silili, An Fara Fadan ‘Yan APC da Suka Hana Osinbajo Samun Takaran 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng