Mafi Yawan Sanatoci Sun Yi Na’am da Yunkurin Tunbuke Buhari Inji Sanatan Bauchi
- Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa yace Sanatoci da-dama sun yi na’am da tsige Shugaban kasa
- Adamu Muhammad Bulkachuwa shi ne Sanata mai wakiltar Arewacin jihar Bauchi a Majalisar Dattawa
- ‘Dan Majalisar yace sun kawo batun tunbuke Muhammadu Buhari ne domin sun kure duka basirarsu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Sanata mai wakiltar Arewacin jihar Bauchi, Adamu Muhammad Bulkachuwa yace akasarin Sanatoci sun goyi bayan a tsige Muhammadu Buhari.
Da aka yi wata hira da shi a gidan talabijin na Channels TV, Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa yace majalisa ta gaza shawo kan matsalar tsaro.
Da yake bayani a wani shirin siyasa a gidan talabijin a ranar Litinin, Sanatan yace bayan an rufe kofa, an tattauna batun tsaro a majalisar dattawan kasar.
Sanata Adamu Bulkachuwa yake cewa ba zai yi magana sosai a kan batun ba, amma mafi yawan Sanatoci sun ga bukatar a fara maganar tunbuke shugaban kasa.
Ba dai 100% ba - Adamu Muhammad Bulkachuwa
The Cable tace da aka yi masa tambaya ko kowa ya goyi bayan hakan, Sanatan yace ba za a iya cewa lamarin ya karbu 100% ba, amma da-dama sun yi na’am.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ba kashi 100 bisa 100 aka amince da shi ba, amma mafi yawa sun goyi bayan haka. Sauran mutane ba su san da wannan ba domin a bayan labule aka yi batun.
Kuma kamar yadda kuka sani, a irin wannan tattaunawa, babu ‘yan jarida, har sauran ma’aikatan majalisa ba su halartar wannan zama – Taron zallar Sanatoci ne.
- Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa
Mun yi duk abin da za mu iya
Jagoran na APC a jihar Bauchi yake cewa ba maganar jam’iyyar APC ake yi ba, ‘yan majalisa sun yi duk abin da za su iya a doka, abu guda ne ya rage ba su yi ba.
Punch ta rahoto Bulkachuwa yana cewa sun yi bakin kokarinsu na ganin an ware kudi kan tsaro, sun bukaci a canza hafsun soji, sun ba shugaban kasa shawara.
“Da muka fahimci duk ba su yi aiki ba, lamarin tsaro na ta tabarbarewa, har maganar kashe kudi bai aiki, sai mu ka fahimci ba mu da ikon aiwatarwa.
“Abin da za mu iya shi ne mu jawo hankalin masu zartarwa cewa abin da ya rage ba mu yi ba shi ne jan kunnensu ta hanyar barazanar mu sauke su.
- Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa
Abin ya jawo rigima
Ganin ‘yan majalisar tarayya sun gagara kawo karshen rashin tsaro a Najeriya, sai suka ba gwamnatin tarayya wa’adin makonni shida domin ganin canji.
A makon da ya gabata aka samu labari rigima ta kaure a zauren majalisar dattawan Najeriya bayan fatali da bukatar tattauna batun tsige shugaban kasa.
Asali: Legit.ng