Gwamna El-Rufai: Zan Tabbata a APC Daga Yanzu Har zuwa Mutuwa ta
- Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya karyata wasu batutuwa da ake yadawa game dashi da siyasarsa
- El-Rufai, a cikin wata hira ya bayyana cewa, ba zai taba barin jam'iyyar APC ba har zuwa karshen rayuwarsa
- Gwamnan na daya daga cikin gwamnonin da ake yawan magana a kansu cikin gwamnonin Najeriya masu tasiri
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa yana daya daga cikin mutane 37 da suka daura tsintsiyar jam’iyyar APC tun farko don haka ya dauki jam’iyyar a matsayin daya daga cikin ‘ya’yansa, rahoton Leadership.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta kai tsaye a gidajen rediyon Kaduna a daren Laraba, ya karyata jita-jitar da ake yadawa na cewa yana shirin sauya sheka zuwa wata jam’iyya, kan batun Tinubu da Shettima.
Yadda Matasa 3 Suka Kama Sana’ar Kosai, Sun Mayar Da Hankali Wajen Ganin Sun Yi Kudi, Hotunansu Ya Yadu
El-Rufai ya sha alwashin ci gaba da kasancewa a jam’iyyar APC har zuwa karshen rayuwarsa, inda ya kara da cewa ‘’idan na bar APC, to na bar siyasa gaba daya’’.
Dalilin da yasa El-Rufai ya cire turar APC a motarsa
Dangane da batun cire tutar APC da ke kan motarsa, gwamnan ya yi karin haske da cewa, ka'ida ne da zarar karfe shida na yamma ta yi, kowace tuta ko dai a sauke ta idan tana kafe a kan sanda, ko kuma a rufe ta idan tana kan abin hawa ne.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnan ya ce wannan ba shi ne karon farko da masu yada jita-jita ke kulla masa makirci ba, inda ya ce:
''Sun ce ina son zama shugaban kasa, sai suka zo suka ce ina so in zama mataimaki a takara, a yanzu kuma sun ce DG kamfen.''
A dai hirar ne jaridar ta Leadership ta kuma ruwaito cewa, El-Rufai ya karyata samun matsayin DG na kamfen din APC.
El-Rufai ya kuma nanata cewa, Muhammad Sani Abdullahi, tsohon kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi, har yanzu shi ne dan takarar jam’iyyar APC na mazabar Kaduna ta tsakiya, inda ya karyata rade-radin da ake yadawa na cewa ya yi shirin korarsa.
A cewarsa, siyasa batu ne na hidima kuma ba ita ce jigon rayuwarsa ba kamar yadda mutane ke tunani.
Sheikh Bello Yabo ya yi addu'ar Allah yasa a sace Buhari, El-Rufai da Garba Shehu
A wani labarin, shahararren malamin addinin musuluncin nan na Sokoto, Bello Yabo, yayi addu'ar Allah ya hada shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu da 'yan ta'adda.
Addu'ar Bello Yabo na zuwa ne kwanaki kadan bayan fitowar wani bidiyo da ya nuna lokacin da 'yan bindiga ke zabgawa wasu da suka sace bulali tare da yin barazanar sace Buhari da El-Rufai.
Garba Shehu ya bayyana martaninsa da ganin bidiyon lakadar fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna, inda ya ce ba komai bane face yada farfaganda.
Asali: Legit.ng