Yadda Matasa 3 Suka Kama Sana’ar Kosai, Sun Mayar Da Hankali Wajen Ganin Sun Yi Kudi, Hotunansu Ya Yadu

Yadda Matasa 3 Suka Kama Sana’ar Kosai, Sun Mayar Da Hankali Wajen Ganin Sun Yi Kudi, Hotunansu Ya Yadu

  • Wani matashi dan Najeriya, Alarma Abd-Karim Isola, ya baje kolin wasu hazikan matasa uku da ke siyar da kosai a bakin hanya
  • Isola ya bayyana cewa yayin da mutane ke tsoron ko matasan na da hatsari, shi ya kan siya kosai a wajensu don sauya wannan tunani
  • Mutane da dama sun yi martani a kan hotunan matasan wadanda suka yi matukar birge su, sun ce su abun koyi ne a cikin al’umma

Wani dan Najeriya mai suna Alarma Abd-Karim Isola a Facebook a ranar Laraba, 27 ga watan Yuli, ya je shafinsa don rubuta labarin wasu hazikan matasa uku a Offa.

Ya ce matasan sun bude sana’ar siyar da kosai sannan suka mayar da hankali a kai. A cewarsa, shekarunsu na a tsakanin 20-25.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Gwamna Zulum Ya Zage Da Kansa Ya Daidaita Cunkoson Jama’a A Wajen Daurin Auren Yar Shettima

Masu siyar da Kosai
Yadda Matasa 3 Suka Kama Sana’ar Kosai, Sun Mayar Da Hankali Wajen Ganin Sun Yi Kudi, Hotunansu Ya Yadu Hoto: Alarma Abd-Karim Isola
Asali: Facebook

Mutane sun zata yan Yahoo ne

Isola ya bayyana cewa matasan wadanda ba yan gari bane sukan kasance cikin kyakkyawan shiga kuma suna faran-faran yayin hulda da abokan cinikinsu. Ya kara da cewa suna dauke da askin da ake yiwa lakani da na ‘Yan Yahoo’.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sanyawa wajen suyar kosansu “akara yahoo” saboda daukar da mutane ke yi masu da farko; cewa suna amfani da sana’ar ne don yin rufa-rufa a kan damfara da asiri.

Kosansu akwai dadi

Don tallafawa kasuwancinsu, Isola ya ce:

“Ina yawan siyan kosai a wajensu don karfafawa mutane gwiwar cewa babu matsala kuma ba sa kwashe arzikin mutane (ban ga laifin kowa ba a kan irin wannan tsoron).”

Ya bayyana cewa kosansu akwai dadi kuma suna yinsa ne cike da tsafta.

Ya kara da cewa:

“A duk sand aka shiga Offa, ka tsaya a gefen Captain Cook sannan ka dandana akara yahoo.”

Kara karanta wannan

Yadda Bidiyon Kyawawan Angwaye Ya Kirkita Mata A Soshiyal Midiya, Wata Tace Angon Take So

Allah ya albarkace su

Debo Adedayo ya ce:

“Wannan abun sha’awa ne! Allah Ubangiji ya albarkaci nemansu.”

Akeem Afolabi ya ce:

“Suna nan a Ibadan, Osogbo da sauransu. Allah ya albarkaci nemansu.”

Abdulkareem Hassan Olayinka ya ce:

“Ina addu’a Allah yasa wannan kasuwanci ya kai su inda suke mafarkin zuwa.”

Sulaimon Blacky ya ce:

“Ku ci gaba da aikin nagari.”

Kin Gama Mun Komai a Rayuwa, Lauya Ya Fashe Da Kuka A Gaban Mahaifiyarsa Kan Dawainiyar Da Ta Yi Da Shi

Agefe guda, wani bidiyo mai taba zuciya da ya yadu a shafukan soshiyal midiya ya nuno wani lauya da aka rantsar a matsayin cikakken lauya yana godiya ga mahaifiyarsa cike da kauna.

A cikin dan gajeren bidiyon, an gano matashin mai suna Harmonihie zube a gaban mahaifiyarsa yana zubar da hawayen murna da godiya.

Matashin ya rike kafafuwan mahaifiyar tasa yayin da yake kuka wiwi, yana godiya gare ta a kan goyon bayan da ta bashi a wannan tafiya na zama lauya.

Kara karanta wannan

An kai wa 'Dan Majalisar Daura, 'Danuwan Shugaba Buhari Hari Har Gida a Katsina

Asali: Legit.ng

Online view pixel