Tsohon Kwamishinan Gwmanan Sokoto Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC
- Ɗaya daga cikin kwamishinonin da gwamna Aminu Tambuwal ya maida kan kujerun su ya sauya sheƙa daga APC zuwa PDP
- Kanal Garba Moyi mai ritaya ya bi sahun shugaban ƙaramar hukuma da wasu Kansiloli da suka koma APC jiya
- Yan siyasa na cigaba da sauya sheƙa daga wannan jam'iyyar zuwa waccan yayin da babban zaɓen 2023 ke ƙaratowa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Sokoto - Tsohon kwamishina a jihar Sokoto kuma babban jigon jam'iyyar PDP, Kanal Garba Moyi (Mai ritaya), ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar All Progressive Congress watau APC.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Moyi ya bi sahun shugaban ƙaramar hukuma da wasu Kansilolinsa Takwas, waɗan da suka koma APC awanni 24 da suka shuɗe.
Garba Moyi na cikin Kwamishinonin da gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya maida kan kujerun su a baya-bayan nan.
Legit.ng ta tattaro cewa Moyi ya kasance Kwamishinan tsaro kafin daga bisani ya yi murabus domin neman tikitin takarar Sanata mai wakiltar Sakkwato ta gabas a majalisar dattawa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yadda APC ta karɓi Kwamishinan
Tsohon kwamishinan ya samu kyakkyawan tarba daga manyan masu faɗa aji na jam'iyyar APC reshen jihar Sokoto ranar Lahadi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Jagoran APC a Sakkwato kuma Sanata mai wakiltar arewacin jihar a majalisar dattawa, Aliyu Magatakardan Wamakko da ɗan takarar mataimakin gwamna karkashin APC, Injiniya Idris Gobir ne suka tarbe shi a gidan Wamakko ranar Lahadi da ƙarfe 9:00 na dare.
A wani labarin na daban kuma Na Kusa Da Gwamna Tambuwal Da Kansiloli Takwas Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
Makusancin Gwamnan jihar Sokoto kuma shugaban karamar hukumar Tangaza, Isah Bashar Kalanjine, ya bar jam'iyyar PDP zuwa APC.
Makusancin Gwamna Tambuwal din ya kara da yin tsarabar kansilolin karamar hukumarsa takwas zuwa jam'iyya mai mulkin kasar nan.
Aliyu Wamakko ya karbe su hannu bibbiyu inda ya tabbatar da cewa za a yi tafiyar tare dasu wurin tabbatar da cigaban Jam'iyyar da jihar baki daya.
Asali: Legit.ng