Za Mu Dawo da Duk Sarakunan da Gwamnatin APC ta tsige Inji Jam’iyyar NNPP
- Suleiman Othman Hunkuyi ya yi alkawarin zai maidawa Sarakunan da aka cire a Kaduna da rawaninsu
- Sanata Suleiman Othman Hunkuyi yace zai janye karin kudin manyan makarantu da aka yi a fadin jihar
- ‘Dan takaran na NNPP ya na sa rai Jam’iyyar hamayyarsa ta lashe zabuka a Kaduna a shekarar 2023
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kaduna - Suleiman Othman Hunkuyi mai neman Gwamna a jihar Kaduna, yace idan jam’iyyar NNPP ta yi nasara, za ta dawo da Sarakunan da aka tunbuke.
A ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli 2022, Daily Trust ta rahoto Suleiman Othman Hunkuyi yana kamfe da Sarakunan da gwamnati mai-ci ta cirewa rawani.
Gwamnatin Nasir El-Rufai ta tsige Hakimai 313 da Masu unguwanni 4, 453 a shekarar 2017 a yunkurin yi wa masarautun da ke jihar Kaduna garambuwal.
Nasir El-Rufai ya fahimci kudin da wadannan Sarakai suke ci ya yi yawa, don haka ya tunbuke su domin gwamnati ta samu kudin da za tayi wa al’umma aiki.
Za mu maida masu rawaninsu - NNPP
Da ya zanta da manema labarai a karshen makon da ya wuce, Sanata Suleiman Othman Hunkuyi yace zai dawo da wadannan mutane da zarar ya shiga ofis.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An rahoto Sanata Suleiman Othman Hunkuyi yana cewa zai yi hakan ne saboda irin rawar da sarakuna ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya a al’umma.
Hunkuyi zai rage kudin makarantu
Hunkuyi ya kara da cewa gwamnatinsu ta NNPP za ta janye karin kudin makarantar da El-Rufai ya yi, yace makarantu ba wuraren samun kudin shiga ba ne.
Har ila yau ‘dan takaran na jam’iyyar NNPP mai adawa ya koka a game da yadda gwamnatin APC ta bar jihar Kaduna da bashin fiye da Naira biliyan 300 a yau.
A cewar Hunkuyi, bashin zai iya zarce wannan adadi idan aka yi la’akari da yadda aka karya Naira. Jaridar Premium Times ta kawo wannan rahoto a jiya.
Muddin NNPP ta kafa gwamnati a jihar Kaduna, Sanata Suleiman Hunkuyi yace zai maida hankali wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake fama da shi.
Tsohon Sanatan ya nuna yana sa ran NNPP za ta karbe mulki a Kaduna a 2023, yake cewa suna da ‘yan takara da za su nemi kujeru 54 da ake da su a fadin jihar.
Musulmi-Musulmi da rigimar APC
Mun fahimci cewa rikicin da ake yi a jam’iyyar APC a kan tikitin Musulmi-Musulmi da aka yi a zaben 2023 ya jawo ana wasan tonon silili na cikin gida.
Ana zargin cewa Babachir Lawal da Yakubu Dogara sun yi wa Bola Tinubu aiki ne a APC, suka hana Yemi Osinbajo samun takara, yanzu suke yin nadama.
Asali: Legit.ng