2023: Babban Sanatan APC Ya Bayyana Abubuwa 2 Da Za Su Hana Tsige Buhari

2023: Babban Sanatan APC Ya Bayyana Abubuwa 2 Da Za Su Hana Tsige Buhari

  • Jigo a jam'iyyar APC ya tofa albarkacin bakinsa kan yunkurin tsige Shugaba Muhammadu Buhari da yan majalisa ke yi
  • A wani hira da aka yi da shi a baya-bayan nan, Sanata Adeseye Ogunleye ya bayyana cewa addini da kabilanci za su hana a tsige Buhari
  • A bangarensu, sanatocin jam'iyyar mai mulki a kasa suna ta kokarin ganin sun dakile yunkurin da yan majalisar na jam'iyyun adawan ke yi na tsige shugaban kasar

Jigo a jam'iyyar APC, Sanata Adeseye Ogunlewe, ya ce dalilai na addini da kabilanci ne za su kawo cikas ga yunkurin da wasu yan majalisar tarayya ke yi na tsige Shugaba Muhammadu Buhari.

Sanatan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a Arise TV a ranar Alhamis 28 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisan APC da-dama na goyon bayan mu Tunbuke Buhari inji Sanatan PDP

Shugaba Buhari.
2023: Sanatan APC Ya Bayyana Dalilai Biyu Da Za Su Hana Tsige Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Ogunlewe, duk da yunkurin yan majalisar marasa rinjaye ke yi don tsige shugaba Muhammadu Buhari, idan yan arewa ba su goyi bayan hakan ba, ba zai yiwu ba.

Sanatan ya ce:

"Ina majalisar a majalisa a matsayin marasa rinjaye a 1993 kuma zan iya tunawa aikin marasa rinjaye daidaita gwamnati idan akwai matsala. Tambayoyi da suka yi da ficewa daga majalisa da suka yi don nuna rashin jin dadinsu da cikin aikinsu ne.
"Duk abin da suka yi dai-dai ne a cikin kundin tsarin mulki amma batun iya tsige shugaban kasa, ba su da rinjaye amma sun bayyana matsayansu kuma koya ya sani."

Sanata Ogunleye ta cigaba da magana kan abubuwan da za su hana yan majalisar nasarar tsige shugaban kasa

Yayin da ya ke tabbatarwa ko abin da Buhari ya aikata saba doka ne, Ogunlewe ya ce:

Kara karanta wannan

An Yi Latti Ma, Tuntuni Ya Kamata A Tsige Buhari, In Ji Sanata Shehu Sani

"Aikin shugaban majalisa Lawan Ahmad yana da muhimmanci sosai. Idan bai gamsu a tsige shi ba, ba zai yiwu ba; shine jagora don haka ba abin da wani zai iya. Suna da babban aiki; ko zai yiwu ko ba zai yiwu ba, ya danganta ga shugaban majalisa.
"Idan ana maganan tsigewa, da ra'ayin yan arewa, wani lamari ne daban. Za su yi taro cikin dare, su sauya abin, saboda suna da rinjaye."

A bangarensu, sanatocin jam'iyyar PDP da galibin yan majalisa wakilai na tarayya sun yarda a tsige Shugaba Buhari saboda kara tabarbarewar tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164