An Yi Latti Ma, Tuntuni Ya Kamata A Tsige Buhari, In Ji Sanata Shehu Sani

An Yi Latti Ma, Tuntuni Ya Kamata A Tsige Buhari, In Ji Sanata Shehu Sani

  • Kwamared Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya goyi bayan yunkurin da sanatocin jam'iyyun adawa ke yi na tsige Shugaba Buhari
  • A cewar Sani, sanatocin ma sun yi jinkiri, tun watanni da dama da suka shude ya kamata su fara shirin na tsige Shugaba Muhammadu Buhari don kam ya gaza
  • Sani ya ce da wuya sanatocin su samu kuri'un da ake bukata domin tsige shugaban kasar amma dai al'ummar kasa za su shaide su a matsayin wadanda suka damu da su

Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa tuntuni ya kamata ace an tsige Shugaba Muhammadu Buhari daga mukaminsa, rahoton The Sun.

Sani ya bayyana hakan ne bayan sanatoci na jam'iyyun adawa, a ranar Laraba 27 ga watan Yuli, sun sanar da cewa sun fara shiri don tsige Buhari saboda tabarbarewar tsaro a kasar.

Shehu Sani
Tuntuni Ya Kamata A Tsige Buhari, In Ji Sanata Shehu Sani. Sanata Shehu Sani. Hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"An yi lattin fara tsige shugaban kasar, tun watanni da suka shude ya kamata ace an fara, Majalisa na da karfin iko a doka ta kira shugaban kasa," Sani ya fada wa Arise TV.

Ya ce sanatocin jam'iyyun masu adawa 'ta yiwu ba za su iya samun adadin kuri'un da za a tsige shugaban kasar ba domin mambobin jam'iyya mai mulki suna ja da baya wurin daukan wannan matakin.'

"Jam'iyyun adawan sune ke da gaskiya. Yan Najeriya za su rika musu kallon wakilan mutanen Najeriya," ya kara da cewa.

Ba rashin kudi ne ya hana a magance matsalar tsaro ba, In ji Sani

Sani ya kuma kara da cewa kallubalen tsaro ba batun rashin kudi bane domin ana bawa hukumomin tsaro da INEC dukkan kudin da suke bukata.

"Cikin shekaru 7 da suka gabata, an ware fiye da Naira Tiriliyan 4.2, amma duk da hakan ba a samu tsaro ba," ya cigaba da cewa "hakan na nuna karara cewa ba a yi amfani da kudin wurin siyan makaman ba ko kuma ba makaman da muke bukata aka siyo ba," in ji shi.

Da ya ke magana kan zanga-zangan ASUU, Sani ya ce a cigaba da zanga-zangar domin idan gwamnati ta damu da bukatun al'umma ya kamata ta warware matsalar na ASUU.

"Muna da kasfin kudi na Naira Tiriliyan 16, idan gwamnati za ta iya biyan tallafin mai na Naira Tiriliyan 7, ya kamata ta ware fiye da haka don ilimi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel