EFCC Ta Yiwa Yan Kasuwar Canjin Dala Dirar Mikiya A Abuja

EFCC Ta Yiwa Yan Kasuwar Canjin Dala Dirar Mikiya A Abuja

  • Jami'an EFCC sun kai wa yan kasuwar canji da ke unguwar Wuse Zone 4 a Abuja samame da nufin kama masu boye dala
  • Hukumar EFCC sun dade suna sa ido kan 'yan canjin dala da ake zargin suna sayen dala don boyewa da kuma fitarwa kasar waje
  • Farashin Naira ya kara faduwa a ranar Alhamis yayin da Dala ya kai naira N705 a kasuwar yan canji

Abuja - Jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawan Najeriya EFCC sun kai wa yan kasuwar canji da ke unguwar Wuse Zone 4 a Abuja samame da nufin kama masu boye dala, kamar yadda Jaridar BBC Ta rawaito.

Rahotanni sun ce EFCC ta dauki matakin kaiwa 'yan kasuwar canji samame ne saboda saya da boye dalar Amurka da suke yi, wanda yana cikin abin dake sa darajar naira na kara faduwa a kwanan nan.

Kara karanta wannan

Yadda Malamar Jami’a Ta Koma Tallan Dankali Saboda Yajin Aikin ASUU

Wata majiya mai karfi ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa samamen ya biyo bayan shirin da hukumar EFCC suka dade suna yi ne.

EFFCC
EFCC Ta Yiwa Yan Kasuwar Canjin Dala Dirar Mikiya A Abuja FOTO CABLE

Hukumar EFCC sun dade suna sa ido kan 'yan canjin dala da ake zargin suna sayen dala don boyewa da kuma fitarwa kasar waje.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

EFCC ta tura jami'anta zuwa manyan filayen jirgin sama na kasa kamar jihar Kano, Legas da Fatakwal da niyyar kama masu kokarin fita da Dala.

A jiya Alhamis ne darajar naira ta kara faduwar da ba ta taba yi ba, inda kimar dala daya ya kai naira N705 a kasuwar yan canji

Kano ta amince da karin kashi 50 na Kudin Tallafin Karatun Dalibai Marasa Galihu

A wani labari kuma, Majalisar zartaswar ta jihar Kano ta amince da karin kashi 50 cikin 100 na alawus din tallafin karatu ga dalibai ‘yan asalin jihar da ke halartar jami’o’in Najeriya. Rahoton TVC NEWS

Ta kuma ba da izinin sakin Naira miliyan 865.4 ga hukumar bayar da tallafin karatu ta jiha a matsayin alawus da ba a biya ba da kuma samar da kayan aiki na biyan dalibai a fadin kananan hukumomin jihar 44 dake masarautu biyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel