Atiku da Tinubu sun Gamu da Cikas, Tsohon Ministan Buhari Yace Shi ne ‘Dan takara
- Chukwuemeka Nwajiuba da Incorporated Trustees of Rights for All International sun kai kara kotu
- Hon. Nwajiuba ya zargi Bola Tinubu da Atiku Abubakar da bada cin hanci a zaben fitar da gwaninsu
- Lauyan tsohon Ministan ya roki Alkali ya hana Tinubu da Atiku yin takara a zaben shugaban kasa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Tsohon Ministan ilmin Najeriya, Chukwuemeka Nwajiuba da wata kungiya sun shigar da kara a kan Asiwaju Bola Tinubu da Alhaji Atiku Abubakar.
Lauyoyin tsohon Ministan da na Incorporated Trustees of Rights for All International suna so a ayyana Chukwuemeka Nwajiuba a matsayin ‘dan takaran APC.
Punch tace an shigar da wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/942/22 ne a kotun tarayya na Abuja.
Mutane shida da ake kara sun hada da jam’iyyun APC da PDP, Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Babban Lauyan Gwamnati da kuma hukumar zabe watau INEC.
Kudi suka yi aiki inji Nwajiuba
Hon. Chukwuemeka Nwajiuba wanda ya saye fam kan N100m amma ya samu kuri’a daya a zaben tsaida ‘dan takarar shugaban kasa, yace an yi amfani da kudi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Nwajiuba ya zargi Bola Tinubu da raba Daloli ga masu tsaida ‘dan takara domin su zabe shi. Daga cikin hujjojinsa shi ne wani faifen bidiyon Rotimi Amaechi.
Rahoton yace a wannan bidiyo an ji yadda tsohon Ministan sufuri watau Rotimi Amaechi ke kokawa a kan yadda aka saida kuri’u a kan wasu kudi kadan.
An sabawa dokar APC da tsarin mulki?
Nwajiuba ya bukaci kotu ta raba gardama a kan yadda aka saba bangarori na 11(A) 12(1) da 13(1) na dokar APC wajen zakulo masu tsaida ‘dan takara a jam’iyya.
Tsohon Ministan ta bakin Lauyoyinsa ya kafa hujja da sashe na 6(6) (A) (B) da (C) da kuma sashe na 15(5) na tsarin mulki wajen hana APC da PDP yin takara.
A karshe tsohon Ministan yace Tinubu da Atiku sun saye kuri’u, sun bada cin hancin Daloli da Nairori saboda su samu tikiti, wanda hakan ya saba dokar kasa.
A dalilin haka, tsohon ‘dan majalisar tarayyan ya bukaci Alkali ya dakatar da Atiku Abubakar da Tinubu daga neman kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Sanatoci za su tsige Buhari
Ku na da labarin wasu Sanatocin jam’iyyar hamayya suna barazanar sauke Shugaban Najeriya a dalilin matsalar tsaro da ta adabbi bangarorin kasar nan.
A cewar Enyinnaya Abaribe, akwai Sanatocin APC mai rinjaye da suke goyon bayan shirin da suke yi na korar Muhammadu Buhari daga fadar Aso Rock Villa.
Asali: Legit.ng