Surukin Bola Tinubu ya fasa-kwai, yace shekarun ‘Dan takaran APC 86 a Duniya
- Shahararren Mai busa sarewa, Tee Mac Omatshola Iseli ya gargadi mutane a kan zaben Bola Tinubu
- Tee Mac Omatshola Iseli ya fito yana cewa ‘Dan takaran na Jam’iyyar APC ya kai shekara 86 a Duniya
- Duk da akwai alakar surukuntaka tsakanin Tee Mac Iseli da Tinubu, ya bada shawarar ka da a zabe shi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Fitaccen makadin nan Tee Mac Omatshola Iseli, ya gargadi mutanen Najeriya a kan zaben Bola Tinubu ya zama shugaban kasa a zaben 2023.
Tee Mac Omatshola Iseli wanda ya taba zama shugaban kungiyar PMAN ta makadan Najeriya, ya zargi Bola Tinubu da boyewa Duniya asalin shekarunsa.
Jaridar This Day ta rahoto Tee Mac Omatshola Iseli yana ikirarin cewa shi surukin ‘dan takaran shugaban kasar ne, kuma yace bai dace da shugabanci ba.
Har ila yau, makadin yace rayuwar tsohon gwamnan na Legas cike take da sirrin da ba a san gaskiyar su ba, ya yi kira ga mutane su guji kada zaben APC.
Makadin ya maida martani ne ga wani mai suna Yemi Olakitan wanda ya yi magana a shafinsa na Facebook, shi yana goyon bayan Tinubu ya samu mulki.
A cewar makadin, babu wanda zai iya yin gamsasshen bayani a game da shekarun Tinubu da asalinsa da kuma yadda ya samu kudin da yake da su a yau.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Maganar Tee Mac Omatshola
“Kowa yana da damar da zai zabi ‘dan takaransa, amma duk mai basira zai tambayi kansa: ‘Na zabi wanda ya dace?’
“Shin wannan mutumi ya cancanta? Ko yana da gaskiya? Ya fada masa gaskiyar shekarunsa da yadda ya samu kudinsa?”
“A shekaru 86 da haihuwa, wannan mutumi yana da lafiyar da zai iya yin mulki a kasar da an yi mata raga-raga?
- Tee Mac Omatshola
Surukin mu ne, amma ba mu tare a 2023
Tee Mac yace ya daina kai wa Tinubu ziyara ne tun da ya tallata Muhammadu Buhari a zaben 2015, yace duk da surukutakarsu, ba zai goyi bayansa ba.
A cewar shahararren makadin. Tinubu surukinsa ne domin kuwa mai dakin ‘dan siyasar, Sanata Remi Tinubu ‘yaruwarsa ce ta bangaren mahaifiya.
“Na daina goyon bayan shi da kai masu ziyara a gida da sauransu lokacin da ya tallata mana Buhari a 2015.”
“Shawarata ga kasar nan ita ce wannan mutum (Bola Tinubu) bai cancanta ya zama shugaban kasar mu ba.”
- Tee Mac Omatshola
A damke Tinubu da Atiku - NNPP
Ku na da labari Jam’iyya mai kayan marmari ta bukaci Jami’an ‘Yan Sanda su damke manyan ‘Yan takara a zaben 2023; Bola Tinubu da Atiku Abubakar.
Shugaban NNPP, Sani Litti yana zargin jam’iyyun da saba doka, ya kuma nemi EFCC ta cafke ‘yan takaran da wadanda suka ba su tutar takara a zaben 2023.
Asali: Legit.ng