2023: Zan fara da tattalin arzikin Najeriya, in yaki rashin tsaro a kwana 100 idan na gaji Buhari, inji Atiku

2023: Zan fara da tattalin arzikin Najeriya, in yaki rashin tsaro a kwana 100 idan na gaji Buhari, inji Atiku

  • Atiku Abubakar da gaske wajen karbar ragamar shugabancin Najeriya a 2023 tare da tsare-tsare masu ban sha'awa ga kasar
  • Dan takarar shugaban kasar a jam’iyyar PDP ya ce zai bunkasa GDPn Najeriya da harkar fitar da kayayyaki zuwa ketare ta hanyar karfafa saka hannun jari a fannin noma
  • Atiku ya kara da cewa kwanaki 100 da zama shugaban kasa zai fitar da kudade da suka kai dalar Amurka biliyan 10 domin fara cimma hakan

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar, ya nuna cewa yana da kyawawan tsare-tsare na ganin Najeriya ta hau saiti idan ya zama shugaban kasa na gaba bayan Buhari.

Daya daga cikin hadiman Atiku kan harkokin yada labarai, Eta Uso, ya bayyana a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 26 ga watan Yuli, Atiku ne "kadai mai tsari", inda ya kara da cewa idan Atiku ya gaji Buhari Najeriya za ta daidaita.

Kara karanta wannan

Muhimmacin Ziyarar Shugaba Buhari Kasar Liberia - Garba Shehu

Abubuwan da zan yi dain na gaji Buhari
2023: Zan fara da tattalin arzikin Najeriya, in yaki rashin tsaro a kwana 100 idan na gaji Buhari, inji Atiku | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Uso ya bayyana hakan ne bayan da tsohon mataimakin shugaban kasar ya ba da cikakken martani ga AbuAmmar Abdullahi, mai goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kan shirinsa na bunkasa harkar noma a Najeriya.

Abdullahi a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce da ya samu dama a wata hira da aka yi da Atiku kwanan nan, da ya tambaye shi shirin da yake dashi na bunkasa GDPn Najeriya da kuma harkar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake mayar da martani, Atiku ya ce idan aka ba shi Najeriya a 2023, zai fara ne da maido da kwarin gwiwar masu zuba jari kan tattalin arzikin Najeriya, ta yadda za su yi kasadar zuba jari musamman a bangaren da ba na mai ba.

A cewarsa, za a iya cimma hakan ta hanyar samar da daidaito da tsari a manufofin tattalin arziki, inda ya ce manufofin za su hankado masu zuba jari zuwa kasar.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi alkawarin yiwa jama'arsa wani abin da Buhari ya gagara yiwa 'yan Najeriya

Atiku ya kara da cewa zai kuma yaki matsalar rashin tsaro.

Na biyu, babban jigon na jam’iyyar PDP ya yi hasashen cewa a cikin kwanaki 100 na farkon mulkinsa, zai kaddamar da Asusun Tallafawa Tattalin Arziki wanda za a zuba wa jarin kusan dalar Amurka biliyan 10.

Ya bayyana cewa asusun zai tallafa wa kamfanoni masu zaman kansu a fannin samar da ababen more rayuwa da kuma ba da fifikon tallafi ga aikin noma, masana'antu a duk sassan tattalin arziki saboda suna ba da gundunmawa mafi girma na samun ci gaba mai dorewa.

Dan siyasar na Arewa ya ci gaba da cewa a fannin noma, gwamnatinsa za ta daukaka harkar noma zuwa wani muhimmin tsari tare da tallafa wa kananan manoma da masu sana’ar noma don noma akalla kashi 10% na filayen noman kasar.

Zabo abokin gami Musulmi: Kwakwalwarsa ta daina aiki, Atiku ya caccaki Tinubu

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sake caccakar abokin hamayyarsa Bola Tinubu na jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Mutane Sun Yi Zaton 'Asirin Kudi' Na Ke Yi Saboda Irin Motar Da Na Ke Hawa, Sanatan Najeriya

Atiku ya caccaki Tinubu kan ikirarin cewa ya ba wa jigon na jam’iyyar APC damar tsayawa takarar mataimakin shugaban kasa a 2007, inda ya ce da gaske Tinubu ne ya nemi hakan, kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito.

Atiku, a wata hira da aka yi da shi a ranar Asabar, 23 ga watan Yuli a gidan talabijin na Arise, ya yi ikirarin cewa Tinubu ya nemi ya yi takarar mataimakinsa a karkashin jam’iyyar Action Congress, tare dashi amma ya ki amincewa saboda ganin hakan ya saba tsarin siyasar addini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.