Obasanjo ga matasa: Kada ku bari tsoffi su sheke gobenku, ku zabi matasa a 2023
- Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya aike da sako mai karfi ga matasan Najeriya gabanin babban zabe na 2023
- Obasanjo ya bukaci matasan da su yi watsi da lakabin "manyan gobe" su karbi mukaman shugabanci a yanzu
- Tsohon shugaban kasar ya yi gargadin cewa idan matasan ba su karbi ragamar mulki a yanzu ba, wasu gurbatattun shugabanni na iya lalata makomarsu ta gobe
Abeokuta, jihar Ogun - Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya kalubalanci matasan Najeriya da su tashi su karbi ragamar shugabancin kasar nan.
Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Asabar, 23 ga watan Yuli yayin wata tattaunawa ta musamman da tsohon tauraron Super Eagles, Segun Odegbami, a gidan rediyon Eagle7 Sports 103.7 FM da ke Abeokuta ta jihar Ogun, inji rahoton Daily Trust.
Kalaman na tsohon shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce na rasa matashi mai tasiri a takarar shugaban kasa gabanin babban zaben 2023.
Ku yi watsi da taken “manyan gobe,” ku karbe kasar nan, Obasanjo ga matasa
Obasanjo ya kuma bayyana cewa ya kamata matasan Najeriya su yi watsi da taken "manyan gobe," yana mai cewa "goben" ba za ta taba zuwa ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce wasu gurbatattun shugabanni za su ruguza abin da ake kira goben matasa idan matasan suka kasa tashi tsaye wajen kwace makomarsu a hannunsu ba.
A cewarsa:
“Shawarata ga matasan Najeriya ita ce, kada ku bari wani ya ce muku ku ne manyan gobe. Idan kuna jiran sai gobe kafin ku karbi ragamar shugabanci, to goben ba za ta zo ba. Za su halaka ta.
"Wannan shine lokaci, matasa su tashi su tabbatar da hakan."
Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi APC a 2023 don samun damar ci gaba da ganin irin ayyukana
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci al’ummar kasar nan da su zabi APC a zabe mai zuwa domin tabbatar da dorewar harkokin siyasa, da kwanciyar hankali a kasar da ma yankin yammacin Afrika, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban ya bayyana haka ne a yau Juma’a a lokacin da yake karbar tawagar daga jihar Nasarawa karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Sule a fadar gwamnati da ke Abuja, a cewar sanarwar da fadarsa ta fitar.
Ya ce zabukan da aka yi a jihohin Anambra, Ekiti da Osun sun tabbatar da kudurin gwamnatinsa na ganin an gudanar da sahihin zabe ba tare da tashin hankali ba.
Asali: Legit.ng